Shugaban Amurka Donald Trump a ranar Talata ya rattaba hannu kan wata doka ta zartaswa da ta janye Washington daga wasu hukumomin Majalisar ɗinkin Duniya da suka hada da Hukumar Kare Haƙƙoƙin ɗan Adam (UNHRC), tare da kafa wani bincike kan kuɗaɗen da Amurka ke ba wa ƙungiyoyi da dama.
Umurnin ya ce, ya janye Washington daga hukumar ta UNHRC da kuma babbar hukumar kula da Falasɗinawa ta MDD (UNRWA), kuma za ta sake duba shiga lamarin da Hukumar Ilimi Kimiyya da Al’adu Majalisar ɗinkin Duniya, wato UNESCO.
An yi wannan yunƙurin ne don nuna adawa da abin da sakataren ma’aikatan fadar White House Will Scharf ya bayyana a matsayin “ƙiyayyar Amurka” a hukumomin Majalisar ɗinkin Duniya.
Mambobi 47 na kwamitin kare haƙƙin bil adama na Majalisar ɗinkin Duniya ne Majalisar ɗinkin Duniya ta zaɓo su zuwa wa’adi na shekaru uku, inda Amurka ke kawo ƙarshen wa’adin ta a ranar 31 ga watan Disamba. A halin yanzu tana da matsayi na masu sa ido a hukumar.
Da alamu dai umurnin na ranar Talata zai kawo ƙarshen duk wata shigar da Amurka ke yi a harkokin majalisar, da suka haɗa da sake duba bayanan kare haƙƙin bil adama na ƙasashen da kuma wasu zarge-zarge na take haƙƙi.
“Dokar ta mayar da hankali ne kan kira da a sake nazarin shigar Amirka da ba da tallafi a Majalisar ɗinkin Duniya bisa la’akari da rarrabuwar kawuna da matakan samar da kuɗaɗe tsakanin ƙasashe daban-daban,” inji Scharf.