Trump ya sha alwashin kawo ƙarshen dokar zama ɗan kasa ga yaran Najeriya da sauran baƙi da aka haifa a Amurka

Zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, ya jaddada alƙawura masu tsauri da ya yi a yaƙin neman zaɓe, na sanya haraji mai tsauri a kasuwanci da kuma korar adadi mai yawa na baƙin da ke zama a Amurka. 

Trump ya tabbatar da hakan ne, yayin da sanar da cewa, zai kawo ƙarshen dokar da ta halastawa baƙi da aka haifa ƙasar zama ‘yan ƙasa na daga ‘ya’yan ‘yan Najeriya da kuma wasu ƙasashe.

A wata hira da aka watsa a ranar Lahadi a gidan rediyon NBC na Meet the Press, Trump ya yi cikakken bayani game da manufarsa ta ɗaukar tsauraran matakai kan shige da fice ba bisa ƙa’ida ba, wanda ya ke da niyyar sanyawa a matakin gaggawa da zaran ya hau kan karagar mulki ranar 20 ga watan Janairu. 

A cewar Reuters, Ma’aikatar Tsaron Cikin Gida ta yi ƙiyasin cewa ya zuwa watan Janairun 2022, sama da mutane miliyan 11 ne ke cikin Amurka ba bisa doka ba, wanda ake ganin da yuwuwar adadin ya haura zuwa yanzu.

Trump ya tabbatar da aniyarsa ta cire duk wani baƙon haure da ya shigo ƙasar ba tare da izini ba, yana mai cewa, “Hukunci ne mai tsauri, amma ya zame mana dole sai mun yi hakan, duba da cewa muna dokoki da ƙa’idojin da ya kamata mu kare martabar su.”

Ya kuma ƙara tabbatar da aniyarshi, inda ya nuna ba gudu ba ja da baya kan wannan ƙudirin nasa, saidai ya ce, da yiwar baƙin haure da aka kawo Amurka ba bisa ka’ida ba tun suna yara su tsira, wanda ya tabbatar za a yi zama na musamman don shawarwarin da za su samar masu mafita.

A lokacin wa’adinsa na farko, Trump ya yi yunƙurin wargaza shirin Deferred Action for Childhood Arriɓals, wanda ke ba da kariya ga ire-iren waɗanan mutane, wanda har ta kai ya yi yunƙurin korar su, saidai Kotun Koli ta taka masa birki.