Tsada da ƙarancin fetur: Mun kusa rufe harkar sufuri – Kamfanonin jiragen sama

Daga AMINA YUSUF ALI

A yanzu haka dai kamfanonin zirga-zirgar jiragen sama na Nijeriya sun bayar da sanarwar yiwuwar su rufe harkokinsu na sufuri nan da kwanaki kaɗan masu zuwa. Kasancewar abokin aikin nasu na sufuri wato man fetur ya yi tsananin ƙaranci kuma farashinsa ya ƙara hauhawar fiye da ƙima. Wato ana sayar da shi a kan farashin Naira 600 kowacce lita guda. 

Allen Onyema, babban jami’in zartarwa na kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na Airpeace shi ya bayyana haka a yayin da yake magana da yawun sauran kamfanonin jiragen saman. Ya bayyana haka a yayin da yake jawabi a gaban kwamitin majalisar dokoki da aka haɗa don yin bincike a game da musabbabin tsada da ƙarancin man jiragen. 

Mista Onyema ya ƙara da cewa, tura ta kai bango, kamfanonin ba su da halin sayen man a kan farashin yanzu. 

Jaridar Businessnews ta bayyana cewa, a yanzu haka matuƙa jirgin sama sun aike da ƙorafi ga gwamnatin tarayya cewa, su gaggauta yin wani abu. Domin daga dukkan alamu man jirgin a nan gaba zai iya kai wa Naira 700 kowacce lita.