Daga AMINA YUSUF ALI
Shugaban rukunin kamfanonin BUA, Abdussamad Rabi’u ya bayyana cewa, safarar kaya daga Chana zuwa Legas ya fi sauƙi matuƙa da araha a kan daga Legas zuwa Kano da ke arewacin Nijeriya.
Abdussamad ya bayyana haka ne a yayin da ya ke yin tsokaci a game da yadda za a sauƙaƙa harkokin sufuri a Nijeriya, musamman ma ɓangaren jirgin ƙasa. Ya yi wannan jawabi ne a garin Faris na ƙasar Faransa.
Inda ya ƙara da cewa, da Nijeriya za ta dage a kan inganta hanyoyin sufuri musamman na jirginƙasa, da ba ƙaramin alfanu hakan zai samar ba ga ƙasar tare da samar da damammaki ba. Daga nan ya yaba wa gwamnatin Buhari a kan ƙoƙarinta game da yadda ta inganta harkar sufurin jirgin ƙasa.
A wannan gaɓar kuma ya yi kira ga ‘yan kasuwa da masu zuba jari a faɗin Duniya da su dubi harkar sufurin jirgin ƙasa a Nijeriya, su yi wani abu a kai. Tunda dai a cewarsa, “muna samar da isasshen abinda zai wadace mu a cikin gida, kuma mu iya fitar da shi zuwa wasu ƙasashen”.
Ya ƙara da cewa, “kamfanin sumuntina na Jahar Sokoto yana iya fitar da sumunti zuwa Jamhuriyar Nijar wacce take da tazarar kilomita 120 daga kamfanin sannan ina kai wa, Ouagadougou ta Burkina Faso, wacce take kilomita 400km daga garin Sokoto.
Sannan ya yi kira ga ƙasar Nijeriya ta kasance mai sarrafa albarkatun ƙasar da Allah ya hore mata. A cewar sa, Nijeriya tana daga ƙasashe guda 12 da Allah ya yi wa baiwar ƙarafa, da kwal da kuma iskar gas. Amma abin takaici tana ɓata maƙudan kuɗaɗe masu ciwo da suka kai dalar Amurka biliyan biyu da rabi domin shigo da ƙarafan da take buƙata a duk shekara.
Amma da a ce za ta kafa masana’antar ƙarafa, da aƙalla za ta samar da ton na ƙarafa kusan miliyan guda da rabi ko ma miliyan biyu a kwacce shekara.