Tsadar farashin DStv da Gotv: Kotu ta haramta wa FCCPC ɗaukar matakin akan MultiChoice

Daga BELLO A. BABAJI

Hukumar FCCPC ta gayyaci Kamfanin MultiChoice Nigeria Limited don yi mata bayani game da dalilan da suka sanya shi yin gyare-gyaren farashi ga hajojinsa a farkon watan Maris, kamar yadda NAN ya ruwaito.

Tun a ranar 27 ga watan Fabrairu ne hukumar ta nemi shugaban kamfanin da ya je ofishinta don gudanar da bincike akan koke-koke da al’umma ke yi game da ƙarin farashin da ya wuce misali.

Haka kuma ta yi wa kamfanin barazanar ɗaukar matakin doka akan sa matuƙar ya gagara bada gamsassun hujjoji game da dalilan da suka sabbaba hauhawar farashin.

A yayin haka ne tawagar shari’a ta kamfanin ta shigar da ƙara a kotun, wanda ke neman a haramta wa FCCPC da jami’anta yi masa barazana da kuma bada umarnin da zai kawo tsaiko ga harkokinsa.

Lauya Onibanjo, wanda shi ne shugaban tawagar lauyoyin kamfanin, ya ce ana gudanar da harkokin kasuwanci ne a Nijeriya ba tare da sanya dokoki ga tsarin farashin abubuwa ba, ya na mai cewa FCCPC a matsayinta na mai aikin bai wa kwastomomi kariya, ba huruminta ba ne kula da tsarin farashi.

Haka kuma, a wata takarda da MultiChoice ya fitar, ya ce kuɗin sabis na hajojin nasa a Nijeriya, shi ne mafi ƙaranci akan yadda ake biya a wasu ƙasashen da ya ke gudanar da harkokinsa, don haka ya ce suna da ƴancin gyara ga farashi la’akari da yanayi.

A lokacin da ya ke sauraron ƙarar, Alƙalin kotun ya umarci FCCPC da ta dakatar da ɗaukar duk wani matakin doka da ta shirya akan kanfanin har zuwa lokacin da za a kammala shari’ar.

Ya kuma ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 27 ga watan Maris.