Daga MOHAMMED ALI a Gombe
Rayuwa a Nijeriya a yau ta kai intaha, yunwa da talauci sun kama gida a duk faɗin ƙasar, sun zama tsumagun cikin gidaje, ba ma na kan hanya ba, musamman gidajen marasa galihu. Daga Gabas da Yamma, zuwa Kudu da kuma Arewa, batun duk ɗaya ne.
Wasu a garin Gombe, kuka suke yi gwamnatin jihohi su bubbufe rumbunan abinci su yi ta raba wa al’umma. Waɗansu kuma kira suke yi da Gwamnatin Tarayya da ta tallafa wa talakawa da “maƙudan kuɗaɗe” ta asusun bankunan su.
Sai dai kuma a nashi martanin, wani Injiniya wanda kuma masanin al’amuran yau da kullum na Nijeriya ne da wasu ƙasashe, mai suna Injiniya Mamman Ibrahim, gani yake yi kafa dokar taɓaci a kan rayuwar ‘yan Nijeriya gabaɗaya, ita ce kawai mafita daga cikin talauci da ƙuncin rayuwar da suka yi shekaru suna ta azabtar da jama’a.
Da yake zantawa da ‘yan jarida a Gombe a makon jiya, Injiniya Mamman ya lura da cewa, kafa dokar tavaci a kan abinci ko akan tsaro da sauransu da Gwamnatin Bola Tinubu ta umarta a yi, sam ba za ta yi wani tasiri ba ga al’umma waɗanda yunwa ta yi katutu a jikunansu.
Da aka tambaye shi ko me yake ganin mafita, sai ya kada baki ya ce, “ai mafita a kafa dokar tavaci a kan rayuwar ‘yan Nijeriya gabaɗaya ita ce sahihin mafita.“
A cewar shi, gwamnati ta tashi tsaye yau ba gobe ba, ta tsayar da duk wasu aikace-aikacenta, ta wadata talakawan Nijeriya da duk nau’in kayan abinci, kayan masarufai da duk ababen more rayuwa da talaka ke buƙata na amfanin yau da kullum, yana mai ƙarawa da cewa to har idan gwamnati ta yi haka tsawon wata ɗaya kawai tana rabawa talakawa kyauta, anguwa-anguwa, gida-gida, za a fara ganin mafita.
Bayan haka, inji shi, gwamnati ta rinƙa shigo da abinci, da kayan masarufi har da magunguna don kiwon lafiya, ta hanyoyin da ta ga sun dace har na tsawon watanni uku tana shishigo da waɗannan ababe, tana kuma bunƙasa na cikin gida ana sayarwa jama’a a farashi ƙalilan da ba zai gagare su ba, bugu da ƙari kuma, ta dage wajen bunkasa noman rani da damina, ta kuma baiwa manoman gaskiya takin zamani da iri da duk abun da zai bunqasa noman ta ko’ina a faɗin Nijeriya, musamman a nan Arewa inda ake da albarkatun filayen noma, a rarraba musu (manoman) kyauta.
Injiniya Mamman yana mai tabbacin cewa, har idan gwamnati ta bi wannan tsarin, ta ci gaba kuma da yin haka, “to kafin shekara mai zuwa za mu rabu da waɗannan yunwa da quncin rayuwa da suka rinqa azabtar da ‘yan ƙasa na tsawon shekaru in Allah ya yarda.
Sai Injiniyan wanda shi ne Shugaban Kamfanin M.M Mechanical Engineering Company, a Unguwa Uku a garin Gombe, ya shawarci Gwamnatin Tarayya har da na jihohi, idan suna so al’ummar Nijeriya su bar kuka da su saboda yunwa da talauci, to dole su rufe ido, su tashi tsaye wajen yaƙi da waɗannan masifu, su dakatar da kome nasu, su duƙufa wajen kawo ƙarshen bala’o’in nan da suke kashe ‘yan Nijeriya a hankali. Gwamnatin Tarayya lalle ta kafa dokar ta ɓaci a kan rayuwar talaka, inji shi.
Daga ƙarshe, Injiniya Mamman sai ya jinjina wa Gwamnan Gombe, Alhaji Muhammad Inuwa Yahaya, a kan katafaren filin kafa sana’o’i da ya gina, yana kuma shawara da cewa, gwamnatin ta baibwa sahihan kamfanoni kawai su saka jari a dandalin mai suna Muhammadu Buhari Industrial Park dake kan babban titin zuwa Daɗin Kowa.