Tsadar rayuwa: Kamfanin MTN zai ƙara kuɗin kira da farashin data

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Kamfanin Telecomms na MTN, ya ce, yana shirin ƙara farashin ayyuka a layinsa saboda hauhawar farashin kayayyaki a wuraren aiki.

An bayyana hakan ne a cikin rahoton kafanin na farko da aka shigar a kasuwar hada-hadar hannayen jari ta Johannesburg a ranar Alhamis.

A hasashen da ta yi na sauran shekarar 2023, kamfanin ya MTN ya ce, “Muna sa ran cewa yanayin kasuwanci a faɗin kasuwanni zai ci gaba da zama ƙalubale har zuwa ƙarshen shekarar 2023 kuma za mu ci gaba da aiwatar da matakan da za mu ɗauka don shawo kan ƙalubalen da ke gabanmu.

Kamfanin sadarwar, wanda ke aiki a cikin ƙasashe 19 da suka haɗa da Afirka ta Kudu, Nijeriya da Ghana, ya ce, haɗewar hauhawar farashin kayayyaki na ci gaba da ƙaruwa kuma ya kai kashi 18.5 cikin 100 a 2023, idan aka kwatanta da kashi 11.5 cikin 100 a 2022.

Kamfanin na MTN ya bayyana cewa, bisa tsarinsa na ‘Ambition 2025’, yana ci gaba da tantance zuba jari, don inganta riba da kuma rage kasada. Don haka, rukunin MTN yana kimanta ficewar ayyuka uku a Afirka ta Yamma bisa tsari cikin matsakaicin lokaci; wato MTN Guinea-Bissau, MTN Guinea-Conakry da MTN Laberiya.

Har ila yau, kamfanin yana shirin ficewa daga Afganistan ta hanyar sayar da hannun jarin MTN ga wani kamfani na M1.

Rahoton ya ce, kuɗaɗen shiga na MTN ya ƙaru da kashi 15.6 zuwa biliyan 53.83 kwatankwacin dalar Amurka biliyan 2.8 a rubu’in farko na shekarar 2023 idan aka kwatanta da dala biliyan 45.69 a rubu’in farko na shekarar 2022, in ji kamfanin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *