Tsaftace amfani da intanet: Kungiyar NADIR ta yi na’am da yunƙurin NITDA

Daga BASHIR ISAH

Ƙungiyar Network of Advocates for Digital Reporting ko kuma NADIR a taƙaice, ta nuna goyon bayanta ga Hukumar Bunƙasa Fasahar Yaɗa Labarai Ƙasa (NITDA) dangane da dokokin da hukunar ta samar don sa ido tare da tsaftace sha’anin yaɗa bayanai ta kwamfuta da intanet.

NADIR ta ce yunƙurin da NITDA ta yi, ta yi shi a kan lokaci musamman ma duba da lokacin zaɓen 2023 irin lokacin da wasu kan yi amfani da intanet wajen yaɗa bayanan ƙarya da na gaskiya.

NADIR ta yi waɗannan bayanan ne cikin wata sanarwar manema labarai da ta fitar mai ɗauke da kwanan wata 19/06/2022 da kuma sa hannun kodinetanta,
Dahiru Mohammed Lawal .

Lawal ya ce saboda muhimmancin harkar intanet ya sa hatta ƙasashen da suka ci gaba ba su bari ana amfani da shi kara zube ba tare da dokoki ba. Don haka ya ce Nijeriya maa bai kamata a bar ta baya ba waajen kwatanta irin hakan.

Ya ƙara da cewa, harkar intanet tana taka muhimmiyar rawa wajen ƙarfafa tattalin arzikin ƙasa kamar yadda aka shaida a 2021.

Daga nan, NADIR ta yi kira ga NITDA da ta yi aiki tuƙuru wajen saka wa ‘yan ƙasa ƙwarin gwiwa gane da ayyukanta ta hanyar yin aiki tare da dukkan waɗanda suka kamata.

Kazalika, NADIR ta buƙaci masu ruwa da tsaki da su ba da tasu gudunmawa wajen tsara waɗannan dokoki don samar da tsare-tsaren da ba za su ci karo da ‘yancin faɗar albarkacin baki ba.

Kungiya ta ƙara da cewa, samar da dokokin zai yi matuƙar tasiri wajen ƙarfafa tattalin arzikin ƙasa wanda hakan zai haifar da ɗimbin aikin yi da kuma sanya ‘yan ƙasa su zama masu bin doka da oda.

Taron manema labaran da NADIR ɗin ta shirya, ya gudana ne a Babban Zauren Taro na PRNigeria da ke Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *