*Isra’ila ta sanar da ci gaba da ɓarin wuta a Gaza
*Shuwagabanin duniya da dama sun yi tir da hukuncin Isra’ila
*An tabbatar da kisan manyan jami’an Hamas biyar
*’Yan Isra’ila na zanga-zangar ƙin jinin cigaba da kai hari a Gaza
Rundunar sojin Isra’ila ta ce za ta ci gaba da kai hare-hare ta sama a Gaza kamar yadda ta fara, wanda a sanadiyyar haka ne hukumomi a Gaza suka bayyana cewa sama da mutum 400 sun rasa rayukansu, ciki har da shugaban ɓangaren tsaro na Hamas.
Kamar yadda BBC ta ruwaito, tuni aka buƙaci fararen hula da ke zaune wasu yankunan Gaza su fice domin tsira da rayukansu.
A cewar Isra’il, ta ɗauki matakin ne bayan Hamas ta ƙi amincewa da sharuɗɗan tsawaita matakin farko na tsagaita wuta a Gaza.
A ɓangaren ƙungiyar Hamas, ta so ne a tafi kai-tsaye zuwa ga mataki na biyu na tsagaita wutar kamar yadda aka tsara.
Wannan hukuncin da Isra’ila ta yanke na ci gaba da ribibin wuta a Gaza bai yi wa ƙasashe da dama daɗi ba inda ƙasashen duniya da dama sun yi tir da ruwan wutar da Isra’ila ta ci gaba da yi a yankin, duk da cewa an sanar da Amurka gabanin ci gaba da kai hare-haren.
Da wannan ne aka samu rahotanni da suka tabbatar da kisan manyan jami’an Hamas har guda biyar. Inda aka bayyana jerin sunayen manyan jami’an Hamas biyar da aka tabbatar da mutuwarsu sanadiyyar ruwan wuta da Isra’ila ta yi a Gaza a cikin dare:
Yasser Harb, wakili a hukumar kula da harkokin siyasa ta Hamas, tare da iyalansa.
Injiniya Issam Al-Da’alis, Shugaban hukumar kula da harkokin siyasa na Hamas.
Manjo Janar Mahmoud Abu Watfa, ƙaramin ministan harkokin cikin gida na Gaza kuma babban jami’in tsaro na Hamas.
Birgediya-Janar Bahjat Abu Sultan, Shugaban hukumar tsaron cikin gida ta Hamas, rundunar tsaro mafi tasiri ta ƙungiyar.
Abu Omar Al-Hattah, ƙaramin ministan shari’a na Gaza.
Haka nan kuma ƙungiyar Palestinian Islamic Jihad PIJ, wato ƙungiya mai ƙawance da Hamas ta tabbatar da mutuwar mai magana da yawunta, Naji Abu Seif, wanda aka fi sani da Abu Hamza.
A ɓangare guda, an ruwaito rashin amincewa da wannan mataki da Isra’ila ta ɗauka daga mutanen ƙasarta, wanda suka fito kwai da kwarkwata don nuna adawa da gwamnatin su na ci gaba da kai hari a Gaza.
Jama’ar ƙasar Isra’ila sun gudanar da zanga-zanga a Isra’ila kan ci gaba da kai hare-hare a Gaza
Isra’ilawan da ake garkuwa da ƴan’uwansu a Gaza sun gana da jagororin siyasa a majalisar dokokin Isra’ila da ke Jerusalem, yayin da wasu dandazon mutane ke zanga-zanga a waje.
Lishi Laɓie-Miran, wadda mata ce ga Omri Miram, mutumin da aka ɗauke a yankin Nahal Oz a ranar 7 ga watan Oktoba, ta faɗa wa ƴanmajalisar a cikin fushi cewar idan har aka kashe mijinta “kada a ɗora mata laifin abin da za ta aikata” idan wani ya nemi “zuwa kusa da ita.”
A wajen ginin majalisar, Samuel, wani sojan ko-ta-kwana kuma malamin tarihi, na daga cikin masu ɗaga murya suna neman a dawo da waɗanda ake garkuwa da su.
Ya ce yana so ya zamo kyakkyawan misali ga ɗalibansa. “Shekarunsu 18, nan da wasu watanni za su shiga aikin soja kuma na yi amannar cewa bai kamata su shiga cikin irin wannan yaƙi ba,” inji shi.
Ya ƙara da cewa, yana ganin akwai siyasa a cikin yaƙin: “Ba batun tsaron Isra’ila ba ne, Benjamin Netanyahu na da tasa manufar game da wannan yaƙin, kuma shi ba mutumin kirki ba ne. Ya kamata a dakatar da yaƙin nan kuma a dawo da mutanen da ake garkuwa da su gida.”
Noga Kaplan, mai shekara 22 a duniya ɗaliba ce a Jam’iar Hebrew, tana riƙe da allo wanda aka rubuta “Dole Bibi ya tafi”
Ta ce, ci gaba da yaƙin “shi ne abu mafi muni da zai faru ga waɗanda ake garkuwa da su” sannan ta yi kira ga gwamnatin Isra’ila da ƙungiyar Hamas da kuma Amurka da su ci gaba da aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta da kuma batun mayar da waɗanda ake garkuwa da su gida.