Tsagaita wutar yaƙin Ukraniya: Trump ya yi wa Rasha barazana da ƙarin farashi

Daga BELLO A. BABAJI

Shugaba Donald Trump na Amurka ya yi wa ƙasar Rasha barazanar sanya mata takunkumi na yin wasu hukunce-hukunce da ƙara farashi a ɓangarori matuƙar ta ƙi amincewa da yarjejeniyar tsagaita wuta a yaƙinta da Ukraniya.

A wani rubutu da aka wallafa a ‘Truth Social’, ranar Juma’a, Trump ya yi wa ƙasashe biyun kiranye da su gaggauta shirya tattaunawa kan dakatar da yaƙin a tsakanin su.

Ya ce, la’akari da yadda ake ƙwarar Ukraniya yayin da ake fafatawa, zai samar da wasu hukunce-hukunce na banki da na wasu ɓangarori da hawar da farashin abubuwa ga Rasha har sai ta amince da yarjejeniyar tsagaita wuta da zaman lafiya.

Ya ja kunnen ƙasashen biyu da su shiga tattaunawa kafin lokaci ya ƙure masu, kamar yadda ya wallafa ba tare da faɗaɗa bayani ba.

Shekaru uku da suka gabata ne tsohon Shugaban Amurka, Joe Biden ya sanya wa Rasha takunkumi a yayin da ta fara yaƙar Ukraniya.

Trump ya aika da saƙon ne sa’o’i kaɗan bayan Rasha ta harba makamai masu linzami guda 261 a yankunan makamashi da ke sassan Ukraniya, kamar yadda hukumomi suka bayyana.