Tsakanin majalisun Nijeriya da CBN kan wa’adin daina amfani da tsoffin kuɗi

Majalisun Nijeriya biyu sun ce suna nan a kan bakansu cewa sai babban bankin ƙasar ya ƙara wa’adin daina amfani da tsoffin takardun naira zuwa watan Yuni.

‘Yan majalisar ta wakilai da dattawa, sun ce kwana goma da Babban Bankin ya ƙara sun yi kaɗan, kuma idan aka ci gaba da tafiya a haka mutane da dama za su talauce.

Tun da farko Babban Bankin ya ce tsoffin kuɗin da suka rage a hannun jama’a yanzu, ba su fi kashi 25 cikin 100 ba, kuma cikin kwana goma ana iya mayar da su bankuna.
Sai dai da alama waɗannan bayanai ba su gamsar da majalisun ba.

Ƙarin kwana 10; Ahmed Bello Umar, daraktan hada-hadar kuɗi na Babban Bankin ya shaidawa manema labarai cewa a halin yanzu dai ba su hana kashe tsoffin kuɗi ba, kawai dai bankuna aka hana su fitar.

Sannan a cewarsa koken da jama’a suka riƙa yi ne suka tursasawa Shugaban Ƙasa amincewa ko umartar a ƙara wa’adi da kwana 10.

Ahmed ya kuma shaida cewa yadda tsarin ya ke shi ne daga 1 ga watan Fabarairu zuwa 10 ga watan, ana sa ran jama’a su kammala sauya kuɗinsu a bankunan.

Sannan sauran kwanaki 7, wato daga 10 ga wata zuwa 17 ga watan Fabarairu, mutum na iya zuwa rassa Babban Banki da ke sassan daban-daban na ƙasar domin sauya kuɗinsu.

“Abin da mu ke son a gane komai ana yin sa ne saboda al’umma wannan ne dalilin da ya sa aka bijiro da hanyoyin da ake ganin zai saukakawa al’umma.

“Sannan a halin yanzu kashi 60 cikin 100 na sabbin kuɗaɗen da ake buƙata akwai su, shi yasa aka ƙara kwanaki 10 wanda tabbas kafin nan kuɗin su wadata a faɗin Nijeriya.

“Ba mu isa mu yi komai ko yanke hukunci ba, ba tare da izinin shugana ƙasa ba, kuma ko a wannan lokaci shi ya bada umarnin a qara wa’adin karɓan tsoffin kuɗin,” inji Ahmed Bello.

Tunzura majalisa:

Sanata Uba Sani wanda shi ne shugaban kwamitin kula da harkokin bankuna na Majalisar Dattijai, ya ce duk waɗannan bayanai ba fa za su yarda ba a majalisa.

Kamar dai takwarorinsa a majalisar wakilai, Sanatan ya ce kwanaki 10 ya yi kaɗan, shi yasa suka yi kudirin da ya buƙaci a tsawaita lokacin daina karvan tsoffin kuɗaɗen zuwa watan shida na shekara ta 2023.

Sanata ya bada dalilansu kan ƙarancin kuɗin da kuma talakawa mazauna karkara da kafin su ɗauko kuɗi zuwa inda akwai bankin lokaci zai kure musu.

Akwai kuma wadanda su kullum sun saba kuɗi na hannunsu, shiyasa yake da buƙatar a yi ƙarin lokaci.

Sanata ya ce, al’umma da suka zaɓe su, su tattauna da su, sun ji kukansu da illolin da hakan ya ke a gare su, shiyasa suka dage kan cewa dole a tsawaita lokaci zuwa watan Yuni.

Ya ce, akwai buƙatarsu ma gwamnoni su tattara kansu bakiɗaya su zauna da shugaban ƙasa, domin tabbatar da cewa sun taimaka wajen nunawa Shugaban ƙasa girman matsalar don a sassauta.

Ya ce, gwamnan Babban Banki ba ya yin abu shi kaɗai kai tsaye ba tare da umarnin shugaban ƙasa ba, don haka zama a fitar da matsaya ne kaɗai mafita.

Sanata ya gargaɗi cewa yin biris da buƙatunsu da sauran al’umma da komai ake yi saboda su, na iya jefa mutane cikin talauci.

Shi ma jagorancin shugaban masu rinjaye na majalisar Alhassan Ado Doguwa, yana mai cewa dole CBN ya yi biyayya da sashe na 20, qaramin kashi na 3, da 4 da kuma 5 na dokar CBN.

Doguwa ya ce, “Wa’adin kwana 10 da CBN din ya ƙara ba mafita ba ne, mu abin da kawai muke buƙata a matsayinmu na ‘yan majalisa shi ne CBN ya yi biyayya ga sashe na 20 ƙaramin kashi na 3 da na 4 da kuma na 5 na dokar CBN”.

“A matsayin Nijeriya na ƙasa mai tasowa, kuma mai bin tafarkin dimokraɗiyya dole mu yi biyayya da abinda doka ta tanadar.

Ya ƙara da cewa, majalisar wakilan za ta bayar da umarnin kamo gwamnan Babban Bankin domin tilasta masa bayyana a gaban kwamitin.

Doguwa ya ci gaba da cewa kwamitinsa zai ci gaba da aiki har sai ya tabbatar da biyan buƙatun ‘yan ƙasar kamar yadda doka ta tanadar.

Yayin da yake bayyana ƙarin wa’adin kwana 10 da cewa ba wani abu ba ne illa yaudarar ‘yan ƙasar tare da ƙara jefa tattalin arzikin ƙasar cikin halin ni-’yasu, Doguwa ya ce dole ne gwamnan Babban Bankin ya bayyana a gaban Majalisar wakilan ko kuma ya fuskancoi barazanar kama shi, ta hanyar yin amfani da ƙarfin da doka ta bai wa majalisar.

Gwamnatin Nijeriya dai tun da farko ta ce ta yanke hukunci sauya kuɗin ƙasar ne domin yaƙi da cin hanci da rashawa.

Wata sanarwa da shugaba Muhammadu Buhari ya fitar na cewa akwai wasu mutane da suka yi amfani da mukamansu wajen voye kuɗaɗen ƙasa, kuma an gano wasu rubabun kuɗaɗe da aka binne a ƙarƙashin ƙasa.

Shi ma Babban Bankin Najeriya CBN ya ce bayanan alƙaluman da yake da su sun nuna cewa ya zuwa watan Octoban 2022 yawan kuɗin da ke voye a hannun mutane a ƙasar ya kai naira tiriliyan biyu da biliyan 700.

Gwamnan CBN ya yi kira ga ’yan Nijeriya da su zama masu biyayya da haɗin kai wajen tabbatar an gama mayar da kuɗaɗen ba tare da wani tashin hankali ba.

Wasiƙa daga MUSTAPHA MUSA, 08168716583.