Tsare-tsarenka masu ma’ana kaɗai ba su wadatar ba – Fayemi ga Tinubu

Daga BELLO A. BABAJI

Tsohon gwamnan Jihar Ekiti, Kayode Fayemi ya ce Shugaba Bola Tinubu yana da kyawawan manufofi ga tsare-tsarensa, saidai hakan bai wadatar ba a jagoranci.

Tsohon gwamnan ya bayyana Shugaba Tinubu a matsayin wa a gare shi, ya na mai cewa lallai ne sai gwamnatin Tinubu ta yi tsarin da zai dace da shugabanci da kuma buƙatar al’ummar Nijeriya.

Fayemi, wanda jigo ne a jami’yyar APC, ya bayyana hakan ne a yayin hira da gidan talabijin na ‘channels’ a ranar Alhamis.

Ya ce waɗanda ke riƙe da mulki sun san gaskiya amma ba za su yi aiki da ita ba saboda waɗansu dalilai da ke shigowa tsakaninsu da waɗanda suke jagoranta.

Ya kuma ce Shugaba Tinubu ya yi kyawawan ayyuka waɗanda dole a bayyana su, ya na mai cewa ya ɗauki matakai masu nauyi da wasu jagorori suka gaza ɗauka.

Saidai, Fayemi ya ce hakan ya jefa al’umma ciki matsanancin yanayi, ya na mai bada misali da cire tallafin fetur da makamantansa.

Ya ƙara da cewa akwai buƙatar a samar da tsari da zai zama maslaha ga ƙasa da al’umma don tafiyar da al’amura cikin yanayi mai sauki.