Tsaro: Arewa ta na kan bom, cewar Bafarawa

Daya daga cikin dattijan Arewa da suke kwana suna tashi cikin tunanin yadda za a shawo kan al’amarin shi ne tsohon Gwamnan Jihar  Sokoto, kuma tsohon xan takarar zama shugaban qasa, Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa (Garkuwan Sokoto), wanda har qasida ya tava gabatarwa ga takwarorin sa manyan yankin kan yadda za a yi a tunkari matsalolin Arewa.

Editocin jaridar Manhaja sun samu damar zantawa da shi domin ya yi mana qarin bayani kan yadda yake ganin za a tubnkari matsalar. A yayin hirar, Bafarawa ya bayyana dalilan da suka sa ya jagoranci tattara alqaluman asarar da aka yi wa arewacin qasar nan daga ta’addancin Boko Haram da masu garkuwa da mutane da satar dabbobi, domin biyan diyya. Haka kuma ya tavo batutuwa da dama da suka hada da matsalolin da yankin na Arewa da kuma yadda za a magance su. Ga yadda hirar ta kasance:

MANHAJA: Ran ka ya dade, Arewa a yau ta samu kan ta a wani hali wanda ba a taba zato ba, har ya zama irin abun nan da ake cewa ana zaton wuta a maqera sai aka sameta a masaqa, domin a lokacin da ake tunanin cewa komai zai daidaita sai kuma abubuwa suka qara dagulewa, duk da xan Arewa ne yake mulkin qasar. Ko me za ka ce?

BAFARAWA: Bismillahir Rahmanir Rahim. To mutane suna ta maganar Arewa, Arewa, shugaban qasar mu dan Arewa, duk abin da yake damun mu shi ne tunanin zai iya faruwa gobe, mu kullum tunanin mu na yau ne. Da mu na da tsari na rayuwa da ba mu samu kan mu yadda muke ba yanzu; duk mai rai ya san akwai rayuwa akwai kuma mutuwa, to babu wani abin da ya kashe Arewa kamar rashin haxin kai, domin sai ka hada kai sannan ka ke tunanin ya za a yi ka gina tafiyar iyalin ka mun samu kan mu tun rasuwar Sa Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato da irin su Tafawa Balewa da Shagari da sauransu, irin su Malam Aminu Kano sa’annan Arewa ba ta samu girgiza ba har lokacin irin su Janar  Hassan Usman Katsina da sauran mutanen da suka tsaya tsayin daka wajen gina Arewa da kishin al’ummar yankin, ba a kuma samu masu cike gurbin su ba. To daga bisani sai aka sa wa ‘yan Arewa matacciyar zuciya, aka sa mana kwadayi da rashin amince wa junan mu, aka sa mana qyashi da hassada da kuma qeta, sannan aka cusa mana ji-ji-da-kai, idan ba kai ka yi abu ba to kowa bai iya ba. Waxannan abubuwa su ne suka hadu suka haifar mana da matsalolin da muke ciki a yanzu. To ana cewa wai shugaban qasa dan Arewa ne amma ba ta canza zane ba, to ai ba shi kadai ke yi ba, saboda tun kafin ma shi Buharin ya zama shugaban qasar menene muka shirya da kan mu cewa idan ya ci zave zai yi mana? Amsar ita ce babu.

MANHAJA: Ina gizo ke saqar kenan?

BAFARAWA: A Shekarar 2002 na rubuta wani littafi mai suna cigaban Arewa A Siyasance, cikin harshen Turanci. Lokacin da na yi littafin na yi shi ne a madadin gwamnonin Arewa gaba daya, a lokacin da muka qaddamar da Qungiyar Dattijan Arewa (ACF), inda na karanta takardar a wurin wannan taron da ya hada duk wani basarake, tsofaffin sojoji da ‘yan sanda da malamai da gwamnoni da duk wani mai faxa a ji da ke Arewa, kuma aka amince akan shi ne littafin da Arewa za ta doru a kai, domin Allah Ya taimake ni ban bar komai ba a cikin littafin, na bayyana yadda za a haxa kai, da kuma yadda Arewa za ta cigaba. Tun ranar da aka ce wannan littafin shi ne zai zama abin koyi ko tsanin mu a nan Arewa ba a sake waiwayar sa ba, aka yi watsi da shi. To alhamdu lillahi, duk sanda ka karanta shi za ka ga cewa yaya aka yi na san waxannan abubuwa. A lokacin na ce in dai ba a bi tsarin da na kawo ba, na ce to tabbas sai an bi gida-gida ana kashe mutane, sai ya kasance yaranmu ba su da makoma. To duk ga shi nan hakan kuwa ke ta aukuwa. 

To ni ba na mamaki wai don an ce shugaban qasa dan Arewa ne; to tun farko me muka gindaya masa ko me muka tsara masa na cewa ga abin da muke so idan ya zama shugaban qasa zai yi mana? Na farko, ya fahimci cewa lokacin da za mu zabe shi ba mu haxa kan mu ba, a makance aka shiga zabe aka ce sai shi, duk sauran qabilu da sassan qasar nan kowanne na da ajandar su. Saboda haka duk abin da ke faruwa yanzu ni ba na mamaki.

MANHAJA: Ka yi gwamna shekara takwas, kuma ka san duk wasu dabarbaru na shawo kan matsaloli, musamman ma harkar tsaro. Akwai wani abu da mutane suke gani kamar lalacewar sarautun gargajiya ne ya haifar da waxannan matsalolin Shin ya ka fahimci abin?

BAFARAWA: To ai basaraken yanzu talaka ne, saboda suna talakawa shi ya sa ake cewa ba su tabuka komai. Ba wai ina kare masarauta ba ne don ta haife ni, a’a, ai sai ka daraja abu yake daraja, mutanen nan da suka zo yanzu ba su dauki masarauta abun girmamawa ba, kuma an wayi gari Gwamna ke nada basarake, to tunda kuwa gwamna ke nadawa ko ya sauke, kuma shi ke fada maka duk wani abu da za ka yi, to ka ga ke nan ba lallai ba ne ya ga girman ka. Shi kuma sarki ya na jin tsoron kada ya yi abin da zai bata wa gwamna rai ya tsige shi. To ka ga tun farko zaben wa zai zama gwamna tun daga nan abubuwa suka lalace. Kafin ka zabi mutum sai ka duba cancantar sa ko rashin cancantar sa kafin ka zabe shi ko kada ka zabe shi. Amma mu duk abin da ya ja mana shi ne farin jinin ka nairar ka, idan kana da naira ba a damuwa da waye ya haife ka, ko daga ina ka ke, ko ba ka da mutunci, matuqar dai kana da kudi to za ka ci zave. To ya sarki zai yi da wannan? Shi dai sarki ba shi da kudin da zai ba mutane, kuma idan aka samu akasi gwamna bai ganin sarkin da daraja, bai mutunta shi, shi kenan za a shiga matsala. Saboda haka maganar wai laifin sarakuna ne wannan ba haka ba ne, domin babu wani abu da sarki zai so in gwamna bai so shi ba.

MANHAJA: Akwai wani abu da mutane suke kallo game da kudaden da ake ba qananan hukumomi wanda suke shiga asusun jiha, har ma sai abin da gwamna ya ga dama yake ba qaramar hukuma, saboda haka sai qananan hukumomin da shugabannin su suka zama kamar hoto, wanda ake ganin kusan hakan ne ya gadar da fatara da kuma talauci a tsakanin jama’a, ba kamar lokacin ku da qananan hukumomi suna tafiya sosai kuma suna aiwatar da ayyuka da kansu. menene ra’ayin ka a kan wannan?

BAFARAWA: To ai waxannan kudade da ka ke fada su ne ginshiqin zaman lafiyar kowace jiha. Aqalla kowace qaramar hukuma za ta samu milyan 100 ko milyan 90. Da kudin nan za su shigo wa shugaban qaramar hukuma ya yi amfani da su cikin talakawan sa; a gyara makarantu da sauran su, a ce kudin suna yawo, to ina mai tabbatar maka da ba mu samu kan mu a halin da muke ciki yanzu ba. Talauci ya taso daga qaramar hukuma, wadannan ‘yan ta’adda su ne masu kudi, su ne masu satar mutane domin a ba su kudin fansa, za ka ga Bafillatani da bindiga a cikin daji, duk wa ke kai masu ita? To da kudaden nan za su riqa zagayawa, za a samu sauqin wannan ta’addanci, amma shi kan shi basarake an bar shi cikin talauci, ga tarin iyali, to ina albashin sa zai riqe shi har ya taimakawa talaka. Saboda haka wannan masifa ta samo asali saboda rashin ba qananan hukumomi cin gashin kan su; idan talakawa suka gane kudin qaramar hukuma su na ga shugaban ai babu zama lafiya tun da ga su ga shi.

To a nan akwai rawar da ku ‘yan jaridu za ku taka na qara wayar da kan talaka ya kuma san ‘yancin sa, a daina cutar sa ko a daina mishi burum-burum, ku riqa nuna musu abu kaza haqqin ku ne, abu kaza an bada bai zo gare ku ba.

MANHAJA: Ran ka ya dade, mu koma batun diyya wanda ka jagoranta, inda ka tattara yawan asarar da Arewa ta yi, ka miqa wa Kakakin Majalisar Dokoki na Tarayya kundin jadawalin asarar da ka bayyana cewa ta kai sama da Naira tiriliyan bakwai. Shin ya a kai ka kai ga wadannan alqaluma kuma me kake fatan ka cimma a cikin wannan gwagwarmaya?

BAFARAWA: To kamar yadda na fada maka mu ‘yan Arewa kullum zindir muke, ba mu tunanin komai sai dai mu tashi mu ce shugaban qasa namu ne, sai mu tsaya tunda muna da uba shi zai yi mana tuwo da miya mu ci mu qoshi.

Ka ga shi wannan kakakin majalisa ne, zabar shi aka yi. Da ya ke suna da ajandar su kuma suna kishin mutanen su, wannan yamutsin da aka yi na EndSars ai su suka hadda abin su kuma ya ci su, sannan suka dawo suka ce a’a ba su yarda ba sai an biya su diyya; mu kuwa ka dubi dubban mutanen mu na Arewa da ake kashewa kullum, da dubban gidajen da ake qonewa, ka dubi marayun da muke da su, mu ba mu ruga mun ce a biya mu diyya ba sai su wadanda ko kwana 30 ba a yi ba da matsalar amma suka ce sai an biya su diyya. Mu kuwa muna zaune mu na jiran banza ba mu tunanin komai.  To da na ga haka sai na ce to ba zai yiwu ba, tunda ga gwamnan Legas can na ga ya hada ‘yan takardun shi ya kai wa shugaban qasa, mu kuwa babu wanda ya shirya nashi ya kai cewar ga masifar da muke ciki, sai ni ma na fara tattara alqaluman domin mu kai, ko dai a bamu tare ko kuma a hana mu gaba daya. To ni wannan tunani na ne, na samu taimako wajen Gwamnan Borno Babagana Umara Zulum, ya bani bayanai da alqaluman asarar da aka yi a jihar sa da irinsu Alhaji Sani Zangon Daura, da Sarkin Birnin Gwari da sauran su, duk na je wajensu na samu bayanai. Amma wallahi da aka ji zan je in kai wa Kakakin majalisa waxannan takardun sai da wasu suka yi qoqarin hana ni kaiwa, kuma wannan abu ni na sa kai na, ban ce wani ya bani ko kwabo ba, haka su ka bi su na ta batawa wai kada in kai wannan rahoton.

To mun je mun kai, na jinjina wa Kakakin majalisa da ya wakilci mutanen sa, shi ma ya jinjina mani. Amma mu ba wannan tiriliyan muke buqata a ba mu ba, ba kudi muke so ba, wannan takarda da na kai a naxa kwamiti su yi bincike su gani gaskiya ne ko qarya ne. Yanzu haka maganar da muke yi mu na da marayu dubu biyar ba su da wurin kwana, ‘yan Arewa ne. Mu ba kudi muke so ba, wadannan marayu a je a gina masu dakunan kwana da makarantun firamare.

Idan ba a yi haka ba nan da shekara biyar, lokacin sun girma sun wuce shiga makaranta, ba su da ilimin boko da na Muhammadiyya, to tabbas su ma za su iya shiga wata sabgar ta daban. Amma wallahi wannan bom ne Arewa take a kai. Duk masifar da muke ciki yanzu wallahi somin-tabi ce, wasan yara ne muddin aka bari wannan bala’i ya ci gaba da faruwa.