Tsaro: Buhari ya ƙaddamar da sabbin jiragen yaƙi guda uku

Daga UMAR M. GOMBE

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da sabbin jiragen yaƙi guda uku ga Rundunar Sojan Sama (NAF).

Jaridar Daily Trust ta ce a ranar Alhamis Buhari ya miƙa jiragen ga rundunar a sansanin sojojin da ke Makurɗi a jihar Binuwai, yayin bikin cikar rundunar shekaru 57 da kafuwa.

Buhari wanda Ministan Tsaro, Bashir Magashi, ya wakilce shi wajen aiwatar da wannan gagarumin aiki ya ce, jiragen yaƙin samfurin JF-17 da aka miƙa wa rundunar hakan zai ƙarfafa wa NAF matuƙa wajen ci gaba da fatattakar ‘yan ta’adda da ta’addanci haɗa da manyan laifukan da ƙasa ke fama da su.

Shugaban ya yi amfani da wannan dama wajen jinjina wa ‘yan Nijeriya bisa turjiyar da suka nuna na ƙin amincewa da ra’ayin masu neman a raba ƙasa.

Yana mai cewa: “Wannan biki na miƙa kayan aikin yana da matuƙar muhimmanci a gare ni, saboda alama ce da ke nuna mun fara cika alƙawuran da gwamnatinmu ta yi na ƙara yawan makamai da kayan aiki ga sojoji da sauran jami’an tsaro.

“Ina kira ga ‘yan Nijeriya da su ci gaba da zama da juna lafiya ba tare da kallon bambancin ƙabila, ko addini ba domin hakan ne zai sanya Nijeriya ta cigaba da zama ƙasa ɗaya dunƙulalliya.”

A nasa ɓangaren, Shugaban NAF, Air Marshal Oladayo Amao, ya bayyana cewa har yanzun ana sa ran samun ƙarin jiragen yaƙi 20 daga watan Yuli na wannan shekarar.

Ya ce, “A ƙarkashin wannan gwamnatin mun samu sabbin jiragen yaƙi guda 23 daga shekarar 2018 zuwa yanzun.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *