Tsaro: Gwamna Dauda Lawal ya haramta haƙar ma’dinai ba bisa ƙa’ida ba a Zamfara

*Ya umurci jami’an tsaro su ɗauki tsattsauran mataki

A yau Asabar, Gwamnan Dauda Lawal, ya sanar da haramta haƙar ma’idanai ba bisa ƙa’ida ba, tare da umurtar jami’an tsaro su ɗauki tsattsauran mataki kan duk wanda aka kama yana aikata hakan.

A tsawon shekaru, haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba na daga cikin abubuwan da ke ta’azzara harkar ‘yan bindiga a faɗin Jihar Zamfara.

Gwamna Lawal, a wata sanarwar manema labarai da mai magana da yawunsa, Sulaiman Bala Idris ya fitar, ya ce gwamnatinsa ta ɗauki wannan matakin ne domin daƙile wannan ɓarna ta haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba, da zimmar kiyaye rayukan al’umma.

Ya ƙara da cewa tuni gwamnatin ta bayar da umurni ga jami’an tsaro da su harbe duk wani wanda aka samu da aikata wannan ɓarna ta haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba.

Ya ce: “Bayar da wannan umurni ya zama dole ne domin kiyaye rayukan al’umman Jihar Zamfara, domin kuma a yi wa ta’asar ‘yan bindiga garanbawul.

“Haka nan kuma mataki ne da zai taimakawa gwamnatin jiha wurin tabbatar da kiyaye arzikinta, tare da rufe ƙofofin ɓarna da suke barazana ga rayuka da dukiyoyin al’umma.

“Haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba na ɗaya daga cikin abubuwan da suke ta’azzara wutar ‘yan bindiga da rashin tsaro. Dole ne mu yi duk wani abu da za mu iya wurin ganin mun magance matsalar tsaro tare da wanzar da zaman lafiya a kowanne lungu da saƙo na Jihar Zamfara.” Inji shi.