Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Gwamnatin Jihar Zamfara ta sauya wa sansanin masu yi wa ƙasa hidima (NYSC) matsuguni daga Ƙaramar Hukumar Tsafe zuwa Gusau, babban birnin jihar, sakamakon matsalar tsaro a sassan jihar.
Manhaja ta ruwaito cewa mataimakin gwamnan jihar, Sanata Hassan Muhammad Nasiha, shi ne ya sanar da haka a lokacin da ya karvi baƙuncin Shugaban Hukumar NYSC Birgediya-Janar M K Fadah.
Har wa yau, ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta yi magana da hukumar NYSC kan dakatar da ayyukan sansanin a jihar sakamakon ƙalubalen tsaro da ya ta’azzara.
Ya bayyana takaicinsa kan koma bayan da aka samu, lamarin da ya sa gwamnan jihar, Bello Muhammad Matawalle ya bayar da umarnin a sauya wa sansanin nan NYSC matsuguni na wucin gadi don ci gaba da gudanar da al’amuransu kamar sauran jiha.
Sai dai kuma Sanata Nasiha ya shaida wa shugaban hukumar cewa a hankali ana samun kwanciyar hankali, jama’a na ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum a jihar.
Mataimakin gwamnan, ya taya Birgediya-Janar M K Fadah murnar naɗin da aka yi mishi a matsayin Darakta-Janar na NYSC, ya kuma tabbatar mishi da ƙudirin gwamnatin jihar na samar da duk abin da ake buƙata domin ɗaukar nauyin sansanin na NYSC na wucin gadi.
A cewar sa, Fadah ya ce sun je jihar ne domin duba wurin da aka samar na wucin gadi da kuma zaɓar wuri mafi dacewa kamar yadda gwamnatin jihar ta amince.
M K Fadah ya ce da hukumar ta ji daɗi kan yadda gwamnatin jihar take nuna damuwa game da sha’anin tsaro.
A cewarsa, ƙalubalen tsaro a yanzu ya zama ruwan dare a kusan kowace ƙasa, ciki har da Nijeriya.