Tsaro: Gwamnatin Zamfara ta buƙaci alummar jihar su ɗauki makamai don kare kai

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Biyo bayan ƙaruwar ‘yan fashi da makami a Jihar Zamfara, gwamnatin jihar ta umurci mutane da su shirya tare da samun bindigogi domin kare kansu daga ‘yan bindigar.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da aka raba wa jaridar Blueprint Sunday, mai ɗauke da sa hannun Kwamishinan Yaɗa Labaran Jihar, Ibrahim Dosara.

A cewar sanarwar, gwamnati ta umurci kwamishinan ‘yan sandan jihar da ya bayar da lasisi ga duk wanda ya cancanta da kuma buƙatar samun irin waɗannan bindigogi domin kare kansu.

“Gwamnati a shirye ta ke ta bai wa mutane dama musamman manoman mu wajen samar da kayan yaƙi na yau da kullum domin kare kansu. Tuni dai gwamnati ta kammala shirin raba fom 500 ga kowace masarautu 19 da ke jihar domin masu son samun bindigogi su kare kansu.”

“Dole ne mutane su nemi izini daga kwamishinan ‘yan sanda, lasisin mallakar bindigogi da sauran makaman da za a yi amfani da su wajen kare kansu”.

Gwamnatin jihar ta bayyana cewa za a kafa sakatariya ko cibiya domin tattara bayanan sirri kan ayyukan masu ba da labari.

“Ana yi wa mutane gargaɗi mai tsauri da nasiha da su tabbatar da cewa duk wani bayani ko bayanan sirri game da mai ba da labari dole ne ya zama gaskiya, domin duk wani bayani kan irin waɗannan bayanan dole ne su kasance da sahihan bayanai kan waɗanda ake zargi, ciki har da hotunansu, sunayensu na gaskiya, adireshi na ƙwarai. sana’a da shaida don shaida gaskiyar bayanin da aka bayar”.

Sanarwar ta ƙara da cewa, gwamnati na ɗaukar matakan hukunta duk wanda aka samu a matsayin mai ba da labari.

Ya ce duk mutumin da ya ba da bayanan da ba daidai ba a kan kowa, za a yi masa hukunci iri ɗaya tare da mai ba da labari kuma za a kula da shi kamar haka.

“Gwamnati ta buƙaci majalisar dokokin jihar da ta yi gaggawar zartar da ƙudurin dokar da ke gabanta, domin bai wa gwamnati damar ɗaukar tsauraran matakai kan masu ba da labari kamar yadda ƙudirin ya kunsa.

A hannu guda, sanarwar ta ƙara da cewa gwamnati ta bayar da umarnin ɗaukar ƙarin jami’an kare al’umma 200 a kowace masarautu 19 na jihar, wanda hakan ya sanya ta zama 500 a kowace masarautu domin ƙara musu ƙarfin gwiwa tare da ƙarfafa ƙarfinta da ƙarfin ta wajen tunkarar barayin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *