Tsaro: Shugaban ƙaramar hukuma ya tsallake rijiya da baya a Sakkwato

Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato

Shugaban ƙaramar hukumar mulkin Gudu, Bello Wakili Bacaka ya bayyana damuwarsa kan yadda ‘yan bindiga ke cigaba da cin karensu babu babbaka a ƙauyukan ƙaramar hukumar mulkin Gudu da ke yammacin Sakkwato.

Bello Wakili ya bayyana damuwar sa ne lokacin wata zantawa da Manhaja, inda ya bayyana cewa a da ana samun hare-hare nan da can, to amma tun a ƙarshen daminar da ta gabata hare-haren ‘yan bindigar suka munana inda ya ce, “kwanan baya ‘yan bindigar sun dirar wa ƙauyen Dageji inda suka ƙone runbunan abinci ƙurmus, sun kashe mutun 3 yayin da biyu suka jikkata muka kai su assibiti, wanda a assibitin ma ɗaya ya rasu daga baya, abin tausayi ma, matar ɗayan wajen gudu fuska ta buge ta rasu nan take.”

A cewarsa ‘yan bindigar kan tare hanya lokaci zuwa lokaci, “akwai lokacin da za su tare dukkanin hanyoyin biyu na Balle zuwa Kurdula, ko kuma Balle zuwa Bachaka.

“Kamar yadda nake gaya maka nan kusa shekaranjiya ina nan aka kira ni aka ce ga ‘yan bindiga can sun tare hanya, kuma dama aikin shi ne ɗaukar mutane ana biyan su kuɗin fansa, kwanan baya ma mutanen Kurdula sai da suka biya miliyan huɗu wajen fansar mutanen ƙauyen da suka yi garkuwa da su su biyar, nan ma kusa akwai wani dattijo da suka ɗauke suka ce sai ya biya miliyan ɗaya da kwalin maganin Tramol biyu, akwai shekaranjiya da zan je gida Bacaka muna tare da sojoji akance mana an buɗe hanya sojoji suka dawo, ina isa wallahi na iske an rufe hanya da motoci uklku ajiye an kama mutanen duk annyi cikin daji dansu, Allah ya taimakeni ko da na isa sun ƙare abinda suke yi, kayan abinci su biskit da sauran su dai na isko duk an yamutse,” inji shi.

Da wakilin Manhaja ya tambaye sa, ƙauyukan da lamarin ya fi addaba, shugaban ƙaramar hukumar mulkin ta Gudu ya bayyana cewa, ƙauyuka da dama ne lamarin ya shafa, kuma daga ciki akwai ƙauyen Tagimba, Ci Maje, Marake, Katsura, Garin Hus, da sauran ƙauyukan balle kusan nan aka fi samun matsalar, a cewarsa.

“Mu kamar a ƙauyukan Bacaka sun taɓa zuwa suka ɗauke mutane, ni kaina sun taɓa yunƙurin ɗauke ɗana amma Allah bai ba su sa’a ba, suka karɓe mashin ɗinsa, sun ka kama wasu mutane cikin su ɗaya ya rasu, sun taɓa zuwa cikin garin Bacaka suka ɗauki mutum uku kuma mutanen sai da kowa ya biya miliyan bibbiyu, amma dai yanzu da sauƙi lamairn ya fi ƙamari ne gefen Balle.”

Matsalar tsaro dai na daga cikin matsalar da ke addabar wasu ƙananan hukumomin Sakkwato, inda ko a lokacin rantsar da sababbin shuwagabannin sai da Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya umarci shuwagabannin da su riƙa gudanar da tarukan tsaro duk bayan mako biyu, lamarin da a cewar shugaban ƙaramar hukumar ta Gudu, ƙamarin da abin ya yi su sukan gudanar da taruklkan ne tun kafin makwanni biyu ma.

“Ko wane sati biyu mukan yi taron tsaro da sarakuna da masu ruwa da tsaki akai, amma kuma da zarar an kai hari nan take za mu kira taron tsaron masu ruwa da tsaki, ka ga kamar shekaranjiya da aka tare hanya biyun da na gaya ma, ni kaina Allah ya tsiratar dabni da yanzu ina hannu, nan kusa sai da na kira taron masu ruwa da tsakin da DPO na ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro, kuma babbar matsalar mu ƙarancin ma’aikata.

“Domin muna magana da DPO gaba ɗaya ƙaramar hukumar mulkin Gudu ‘yan sanda 26 gare mu, kuma gunduma uku na uwayen ƙasa garemu ko Balle suna iya karewa balle sauran wasu wurare, sannan gefen sojoji motoci biyu gare su, ɗayar ma ta tsufa, don an kai wani hari da na kirasu ce min suka yi motar su guda cikin yashi ta kahe sai da sunka koma turin ta, to soja ya koma turin mota wace aka yi?”

Bisa wannan ne ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta samar masu da ƙarin jami’an tsaro musamman ma na sojojin da ‘yan sanda, domin a cewar sa ɗaukacin ƙaramar hukumar Gudu da wani sashen ta ke maƙwabtaka da Jamhuriyar Nijar nabda ‘yan sanda 26 ne kawai!

“Don Allah a duba halin da muke ciki na matsalar tsaro a samar mana da mafita, in kuma abu mai yiwuwa ne don Allah a ba mu bindigogi a ba soji su kula da mu in za a fita a samu ‘yan banga a ba su, har da ni mu shiga daji, kuma dama nakan shiga daji”.