Tsaro: Shugaban jaridun Manhaja da Blueprint ya buƙaci a kyautata alaƙa tsakanin kafafen yaɗa labarai da gwamnati

Daga AISHA ASAS

Shugaban jaridun Manhaja da Blueprint, Alhaji Mohammed Idris Malagi, ya yi kira da a ƙarfafa haɗin gwiwa da yin aiki tare tsakanin kafafen yaɗa labarai da kuma gwamnati wajen daƙile matsalolin tsaron da suka addabi ƙasa.

Alhaji Idris ya yi wannan kira ne a wajen taron makon ‘yan jarida wanda Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Ƙasa (NUJ) Reshen Jihar Neja ta gudanar ranar Asabar a Minna, babban birnin jihar.

A matsayinsa na babban baƙo mai jawabi a wajen bikin, inda ya yi bayani a kan batun: Kafafen Yaɗa Labarai da Matsalar Tsaro a Nijeriya: Lamari da ya Shafi Jihar Neja, ya bayyana irin rawar da kafafen yaɗa labarai kan taka wajen agaza wa gwamnati a fagen yaƙi da matalar tsaro a ƙasa.

Ya ce, “Kafafen yaɗa labarai na da muhimmiyar rawar da za su taka wajen gwagwarmayar yaƙi da matsalar da ba ta bar yaro ba balle babba wajen hana su barci idanunsu biyu a rufe.

Da yake magana ta bakin wakilinsa, tsohon Sakataren Labarai ga Gwamnan Neja kuma Editan Labarun Harkokin Tsaro na Jaridar Blueprint, Jibrin Baba Ndace, Idris ya ce, “Domin iya tunkarar wannan matsalar ta tsaro yadda ya kamata a ƙasar nan dole ne sai ɓangarorin yaɗa labarai, gwamnati hukumomin tsaro a dukkanin matakai da su kansu ‘yan ƙasa, an haɗa hannu.”

Da wannan ne ma ya yi kira na musamman ga ‘yan jaridu da ke ɗauko rahotannin da suka jiɓanci fannin tsaro da su zao masu kulawa tare da yin aiki daidai da ƙa’idojin aiki ba tare da bada bayanan da za su haifar wa fannin tsaron ƙasa cikas ba.

Ya ce, “Bisa la’akari da irin ‘yancin walwalar da ‘yan jarida da kafafen yaɗa labarai ke da shi, suna da ƙarfin faɗa a ji. Baya ga al’adun ilimantarwa, faɗakarwa, nishaɗantarwa da aka san su da su, ‘yan jaridu suna taka rawar masu sanya wa al’umma idanu kan yadda harkokin al’umma da na gwammnati suke gudana.”

Ya ci gaba daa cewa, “Dole ne kafafen yaɗa labarai da al’umma su miƙe su yaƙi ƙalubalan tsaron da ke ta ƙaruwa a ƙasa ta hanyar ɗaukar matakan sadarwa da suka dace wajen daƙile matsalar tsaro a cikin al’umma.”

Daga nan ya yi kira ga ‘yan jaridu da sauran ma’aikata a kafofin yaɗa labarai da su himmantu wajen aiwatar da aikin jarida wanda al’umma za ta amfana da shi tare da yin amfani da kafafen yaɗa labarai a matsayin hanyar tallafa wa ƙoƙarin ma’aikatan yaɗa labarai wajen yaƙi da matsalar tsaron ƙasar nan.”

Alhaji Idris wanda shi ke riƙe da muƙamin Babban Sakataren Ƙungiyar Masu Buga Jaridu ta Nijeriya (NPAN), ya bada shawar cewa za a iya inganta damarmakin da kafafen yaɗa labarai ke da su wajen isar da saƙo yadda ya kamata ta hanyar shirya tarurrukan ƙara wa juna ilimi a-kai-a-kai da kuma bunƙasa sanin makamar aiki.

Tare da nuna buƙatar da ke akwai dukkan masu ruwa da tsaki a fannin tsaro su san irin ƙoƙarin da kafafen yaɗa labarai ke yi wajen bada gudunmawarsu ga sha’anin yaƙi da matsalolin tsaro.

Daga nan ya bada shawarar ana iya bunƙasa harkokin kafafen yaɗa labarai ta hanyar shirya tarurrukan ƙara wa juna ilimi a-kai-a-kai. Sanna wajibi ne dukkan masu ruwa da tsaki a fannin tsaro su san da kafafen yaɗa labarai a matsayin abokan tafiya don lalubo hanyoyin da suka fi dacewa a bi wajen kawar da matsalolin tsaron ƙasa.

Domin cim ma wannan ƙudiri kuwa, ya ce ya zama wajibi a buɗa hanyoyin samun muhimman bayanai ga kafafen yaɗa labarai da su kansu ‘yan jaridu da gwamnati da sauransu.

Alhaji Idris ya ce, “Da na shiga harkar wallafa jarida, inda na soma da mujallar nan ta The Market Magazine, wadda ita ce mujallar ta farko a Nijeriya mai yaɗa harkokin kasuwanci da tattalin arziki, burina a bayyane yake, wato samar da wata dangantaka a tsakanin gwamnati da kuma ɓangaren ‘yan kasuwa masu zaman kansu don amfanin Nijeriya.”

“Sannan na zo na soma wallafa jaridar Blueprint, duka dai da zummar ƙarfafa haɗin kan ƙasa, inda muka sanya burinmu ya zama dawo da kyakkyawan tsammani na kiyaye rayuka a cikin zukatan al’umma. Ta hanyar tabbatar da cewa waɗannan jaridu ana wallafa su bisa ƙa’idojin da suka dace da kuma sanin makamar aiki.

“Ba mu tsaya nan ba, domin ƙara ƙaimi ga dimukuraɗiyyarmu da kuma haɗin kan ƙasa, sai muka ƙirƙiro jaridar Blueprint ta Hausa mai suna Blueprint Manhaja, mu ke da tashar rediyon nan ta WeFM 106.3, sannan mun samu lasisin kafa gidan talabijin na Blueprint Television.

Daga bisani, Kakakin Nupen ya yi kira ga gwamnatoci da hukumomin tsaro da su ci gaba da samun ƙwarin gwiwa kan ‘yan jaridu a fagen tattalin bayanan tsaro. Tare da jaddada cewa, “lamarin tsaro abu ne da ya shafi kowa, don haka ya zama wajibi jami’an tsaro su ci gaba da rungumar ‘yan jarida wajen yaƙi da matsalolin tsaro.

“Ina da yaƙinin cewa nan ba da daɗewa ba za mu koma kamar yadda aka san mu da zaman lafiya a can baya. Ba yau ne matsalolin nan suka soma ba, don haka kuskure ne ɗora laifin hakan kan wata gwamnati. Maimakon haka, kamata ya yi mu haɗa kai wajen kawar da waɗannan matsaloli a matsayinmu na ƙasa.”

A matsayinsa na babban mai ƙaddamarwa na kalandar ‘Almanac” da ƙungiyar ta buga, Alhaji Idris Malagi ya bada gudunmawa ta kuɗi na milyan N1. Sannan ya yaba wa NUJ ta jihar bisa ƙoƙarin da ta yi wajen shirya wanna taro a daidai wannan lokaci da kuma zaɓen taken da ya dace.

Daga cikin waɗanda suka halarci bikin har da wakilin Gwamnan Neja Alhaji Abubakar Sani Bello, ( Alh Yusif Suleiman, Kwamishinan Albarkatun Ruwa na Neja), Shugaban Ƙungiyar ‘Yan Jarida na Ƙasa, Mr. Chris Isiguzo, Shugaban NUJ reshen Jihar Neja, Mal. Abdul Idris, wakilin Shugaban Taro, Engr Sani Ndanusa, Marafa Nupe ( MaL Mohammed She, kuma Ma’aji na ƙasa na NUJ).

Sauran su ne, wakiliyar Mataimakiyar Babban Bankin Nijeriya, Hajiya Aisha Ahmed, (Dr Zainab Ndanusa), Alh. Muhammad Kudu Usman – Daraktan Sashen Kuɗi da Gudanarwa a Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya, Alh. UT Usman, Darakta Janar na Hukumar Fansho ta Neja, Alh Danladi Buhari da dai sauransu.