Tsaro: Tambuwal ya ziyarci Babban Sufeton ‘Yan Sanda na Ƙasa

Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato

A wani mataki na daƙile matsalar rashin tsaron da ya ta’azzara a wasu sassan Jihar Sakkwato, gwamnan jihar Aminu Waziri Tambuwal ya ziyarci babban Sufeton ‘yan sanda na ƙasa, Usman Alkali Baba a hedikwatar rundunar da ke Abuja, babban birnin tarayya, Abuja.

Ziyarar dai na da manufar ƙara danƙon zumunci tsakanin gwamnatin jihar da rundunar ‘yan sandan Nijeriya, ta yi nazari a kan ɓangarori da dama, da ma yadda za a dunƙule kan nasarorin da ake samu a halin yanzu na yaƙi da ‘yan fashi da garkuwa da mutane da sauran laifuka a jihar.

Gwamna Tambuwal, wanda ya yaba da ƙoƙarin jami’an rundunar, ya kuma yaba wa IGP bisa goyon bayan da yake bai wa gwamnatin jihar a ƙoƙarinta na ganin an shawo kan ƙalubalen rashin tsaro.

Gwamnan ya kuma nuna godiya ga IGP ɗin tare da yaba masa bisa ci gaba da haɗin gwiwa tsakanin ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro a jihar tare da kira ga rundunar da ta ƙara zage damtse wajen wanzar da zaman lafiya a sassan da ke fama da matsalar tsaro.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *