Tsofaffin ɗaliban Kwalejin Kanta suna taka muhimmiyar rawa

Daga JAMIL GULMA a Kebbi

Shugaban makarantar Kwalejin Kanta da ke Argungu a jihar Kebbi, Malam Hassan Yakubu ya yaba wa ƙungiyar tsofaffin ɗalibai bisa ga irin rawar da su ke takawa wajen kulawa da makarantar.
Ya yi wannan bayani ne ranar Litinin ɗin da ta gabata a wajen taron shekara-shekara da ake gudanarwa a harabar makarantar.

Malam Yakubu ya ce ya zama dole hukumar wannan makarantar ta yaba wa wannan ƙungiyar saboda a duk lokacin da wata buƙata ta taso tun kama daga shawara ya zuwa aikin ƙarfi da na  aljihu duk wanda aka kira domin gudunmawa yakan hanzarta aiwatar da abinda ake buƙata wanda yana ɗaya daga cikin abubuwan da suka sanya wannan makarantar ta kawo a wannan matsayin da ta ke.

Haka zalika ya yaba wa ƙungiyar malamai da iyaye saboda su ma ba bar su a baya ba wajen bayar da ta su gudunmawa.

A ɗaya ɓangaren kuma Malam Hassan Yakubu ya koka bisa ga yawan sace-sace da ke zama babbar matsala ga ɗalibai sanadiyyar faɗuwar da ginin da aka  zagaye makarantar ya yi sannan kuma akwai buƙatar ƙarin maau gadi saboda duk faɗin makarantar masu gadi uku kacal ke akwai su ke aiki dare da rana.

Ya ƙara da cewa a cikin zangonnin da suka gabata ɗalibai sun kashe wani ɓarawo da ya shigo don yi musu sata wanda Allah kaɗai ya kiyaye da abin ya zamo babbar matsala tsakanin ɗalibai da mutanen gari.

Ya Kuma yi tuni ga gwamnatin jihar Kebbi ƙarƙashin jagorancin Maigirma Gwamna Sanata Atiku Bagudu bisa ga alƙawarin da ya yi nazagaye harabar makarantar lokacin wani bukin murnar cikar makarantar shekaru hamsin da aka gudanar shekarar da ta gabata.

Tun farko da ya ke jawabi shugaban ƙungiyar tsofaffin ɗaliban na ƙasa Alhaji Muhammadu Sani Aliero bayan sakon barka da zuwa, ya yuma yi addu’ar Allah ya jiƙan marigaya daga cikinsu, ya kuma gode wa Allah da ya ba su damar halartar wannan taron da ya ke shekarar 2019  ba a samu yin taron ba sanadiyyar Covid-19.

Ya bayyana kaɗan daga cikin nasarorin da aka samu da suka haɗa da sabunta ƙofar makarantar da Faruk Ahmed (1984) ya yi, gyaran ɗakunan kwanan ɗalibai uku da suka haɗa da Yarima House, Nabame House da kuma Surami House, gyara wajen wasannin ɗalibai. Gyarawa tare da samar da wadataccen ruwa ga ɗalibai da gidajen malamai, gyara ɗakin shan magani, samarwa da kuma gyara banɗakuna.

Gina ɗakin taro da samar da kujeru daga Yakubu Muhammed Argungu ɗan shekarar 1983, samar da nau’rori a cibiyar bincike ta zamani daga Farfesa Muhammed Isah ɗan shekarar 1983.

Aliero ya ƙara da cewa yanzu haka an ɗora wa kowane ɗalibi da ya bayar da Naira dubu ɗaya kowace shekara domin samun kuɗin shiga, inda kuma aka buƙaci mawadata daga cikinsu za su biyan fiye da haka.

Ya yi godiya ta musamman ga Alhaji Yusuf Haruna Rasheed (Sardaunan Gwandu) bisa ga gudunmawar Naira milliyan biyu da kuma Alhaji Haliru Abubakar Gwandu (mataimakin babban sufeton ‘yan sanda) da ya bayar da Naira dubu ɗari biyar lokacin babban taro da aka gudanar.

Daga ƙarshe ya yaba wa wannan ƙungiyar bisa ga irin gudunmawar da ta ke bayarwa a duk lokacin buƙatar hakan ta taso musamman haka-zalika ba za su manta da Sanata Dr. Yahaya Abubakar Abdullahi (Mallamawan Kabi) kuma shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa bisa ga gyara ɗakunan kwanan ɗalibai na Kebbi House da kuma azuzuwa goma sha biyu wanda bayan ya gyara kuma ya samar da katifu da gadaje da kuma kujeru ta hanyar Alhaji Sama’ila Dantagago ɗan shekarar 1998.

Taron dai ya samu halartar tsofaffin ɗalibai tun daga shekarar 1969 zuwa yau daga sassa daban-daban daga Nijeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *