Tsoffin ɗaliban Kwalejin Sa’adu Rimi na ‘yan ajin 92 sun yi taron cika shekara 30 da kammalawa

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

Tsofaffin ɗalibai na Kwalejin Ilimi ta Sa’adu Rimi da ke Kano Kano, ‘yan ajin 1992 sun yi taron cika shekaru 30 da kammala makarantar.

Taron wanda aka yi a ranar Lahadi a ɗakin taro dake harabar kwalejin ya samu halartar ɗimbin tsofaffin ɗaliban da wasu daga cikin malamai da suka koyar da su.

Da yake bayani akan maƙasudin taron, shugaban riƙo na ƙungiyar, Mai Shari’a Kamilu mai Sikeli ya ce ƙungiyar ta samo asali ne daga gama makarantar saboda ba sa haɗuwa da juna sai in wani abu ya taso ko a ɗaurin aure ko wajen ta’aziyyar rasuwa, inda suka akwai buƙatar lallai su zo su haxa kawunansu ko ba komai a haɗu a gaisa a yi zumunci, wannan ne a cewarsa ya sa suka fara irin wannan taro tun shekaru bakwai da suka gabata.

Ya ce babban burinsu shi ne na haɗin kai da zumunci da kuma taimaka wa masu ƙaramin ƙarfi da iyalan waɗanda suka rigasu gidan gaskiya na ƙungiyar tsoffin ɗaliban.

Mai Shari’a Kamilu mai Sikeli ya ce hatta malamai na kwalejin sun yaba da taron saboda suma ana ƙulla musu zumunci tsakaninsu da waɗanda suka yi aiki tare.

Kamilu ya yi kira ga shugabanni na kowane mataki a ƙasar nan su bai wa ilimi muhimmanci fiye da komai domin duk al’ummar da babu ilimi a cikinta karyayyiya ce babu ita. Sun kuma nuna goyon bayan su na a bai wa ilimi fifiko fiye da komai a rayuwa.

Shugaban tsofaffin ɗaliban ‘yan aji na 92 na kwalejin ilimin na Kano ya ce yana tuna yadda suka sa kansu a makaranta ba tare da tilastawar iyayensu ba suka bar gidajensu ba don ba su da shi ba suka zo suka kama ɗakunan haya suka yi rayuwa ta karatu za su yi girki tare su kwana a ɗaki ɗaya su tashi wannan abu in ya tuna yana ba shi sha’awa da jin daɗi.

A yayin taron dai an miƙa shaidar karramawa ga wasu daga cikin malaman kwalejin da ɗaliban bisa irin gudunmuwar da suke bai wa cigaban ilimi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *