Tsoffin ɗaliban sakandiren Gwarzo sun yi taron jaddada zumunci

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

Ƙungiyar Tsofaffin Daliban Makarantar Sakandire ta Gwarzo sun gudanarda taron sada zumunci.

Shugaban ƙungiyar, Alhaji Bashir Abba Shariff a yayin taron da aka yi a ɗakin karatu na Murtala Muhammad ya ce basu tava haɗuwa irin na wannan lokacin ba, domin duk wanda suka rage a raye, sun zo taron daga sassa daban-daban na kiasar nan harma akwai wanda yazo daga ƙasar Ghana.

Ya ce, maƙasudin taron shine don a farfaɗo da dangantaka ta asali mai ɗorewa a tsakaninsu dan ta cigaba da yaɗo duk da cewa kusan kaso 27 na daga cikinsu sun rasu, amma abin jin daɗin wanda suka rage kowa ya zo taron.

Ya yi nuni da cewa, samada shekara 53 da gama makarantar wasu ma tunda suka bar makarantar ba su haɗu dasu ba,sai a wannan haɗuwa rabonsu da ganin juna tun sunasa gajeren wando.

Ya yi nuni da cewa babban abinda ya fi faranta masa rai a taron shine haɗuwarsu duk da cewa waya kawai ya ɗauka ya kirawosu kuma suka amsa.

Ya ce, a matsayinsu na tsofaffin ɗaliban Sakandiren ta Gwarzo sun sa anyi rijiyar burtsatse an ja fanfo an wadatar da ruwa, sannan sun kai kwamfitoci da sauran gine-gine a makarantar.

Shugaban ƙungiyar na tsofaffin ɗalibai na farko na sakandiren Gwarzo ya yi nuni da cewa ingancin ilimi da aka baiwa ɗalibai a lokacinsu yafi na yanzu dan yanda rayuwa ta sauya ko mangwaron da ya fi na yanzu inganci.

Ya yi nuni da cewa Gwamnati na yin ƙoƙarinta kuma su al’umma yakamata su taimaka maganar karatu yanzu ba za a ce yana hannun Gwamnati kawai ba, dole mutane su sa hannu dole sai mutane sun shigo sun taimaka wajen ilimi, da tarbiyyar ’ya’yansu da ta lafiyarsu.

Bashir Abba Sharif yace in ana maganar ilimi ba a hannun Gwamnati kawai yake ba,dole sai mutane sun shiga,wanda za ka ilmantarma sai ya zo ya yarda cewa yana buƙatar ilimin, dan kyautata cigaban rayuwarsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *