Daga BASHIR ISAH
Rahotanni sun ce Bello Musa Ƙofarmata ya rasu ne ranar Talata a mahaifarsa, Kano yana da shekara 34.
Tuni aka yi jana’izar marigayin a Kano daidai da karantarwar Musulunci.
Bayanai sun nuna Musa ya soma harkar ƙwallon ƙafa ne a 2007 a kulob ɗin Buffalo da ke Kano, daga bisani ya samu shiga ƙungiyar Kano Pillars.
A 2010 ya sauya sheƙa zuwa ƙungiyar Heartland a Owerri sannan ya sake dawowa Kano Pillars a 2012, kana daga bisani ya tafi ƙungiyar Elkanemi Warriors a Maiduguri.
Bayan wasu lokuta marigayin ya samu kwantiragi da kulob ɗin IK Start a ƙasar Norway.
Ya samu nasarori da dama a fagen ƙwallon ƙafa a halin rayuwarsa.