
Iwuoha ya bar duniya yana da shekara 68 bayan fama da ya yi da ciwon suga na tsawon lokaci.
Shugaban Ƙungiyar ‘Yan Wasan Fina-finai na Nijeriya, Ejezie Emeka Rollas, shi ne ya tabbatar da mutuwar marigayin.
Kana ya yi amfani da wannan dama wajen jajanta wa iyalan marigayin game da rashin.