
Daga BELLO A. BABAJI
An sanya sunan tsohon ɗan wasan Nijeriya, Ismail Taye Taiwo a cikin jeren ƴan wasan da suka fi girman daraja a kundin tarihi na ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Marseille dake ƙasar Faransa.
Marseille ta wallafa hakan ne a shafinta na sada zumunta inda ta ce tsohon ɗan wasan ya shiga kundin ‘OMLegends club’.
Taiwo ya koma Marseille ne a watan Junairun shekarar 2005 a matsayin ɗan wasan baya gefen hagu, daga wata ƙungiya a firimiyar Nijeriya.
Ɗan wasan mai shekaru 39 ya buga wa Marseille wasanni 271 inda ya zura ƙwallaye 25 da bada wasu 23 da aka ci.
Ya kuma taimaka wa ƙungiyar a nasarorin da ta yi na lashe gasar Ligue 1 da French League Cup da kuma French Super Cup a zamansa da ita.
A shekarar 2011 ne ya sauya sheƙa zuwa ƙungiyar AC Milan.