Tsohon ɗan Majalisar Tarayya ya zama hadimin Aisha Buhari

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya naɗa Hon. Sani Zorro a matsayin Babban mai taimaka masa na musamman a kan Dabarun Hulɗa da Jama’a a ofishin Matar Shugaban Ƙasa.

Sabon babban mai taimakawa na musamman a Ofishin matar shugaban ƙasa, Muhammad Sani Zorro dai ƙwararren ɗan jarida ne kuma jagora a aikin jarida a Nijeriya, Afirka, da ma duniya.

Babban mai taimaka wa Shugaban Ƙasa a kan harkar yaɗa labarai, Garba Shehu ne ya tabbatar da naɗin a wata sanarwar da ya fitar a Asabar da ta gabata a Abuja.

Shehu ya ce Zorro zai yi amfani da ɗumbin ƙwarewarsa a aikin jarida ta shekara da shekaru, inda ya yi wallafe-wallafe da dama sannan ya riƙe muƙaman ƙungiya a matakai daban-daban,

Ya ƙara da cewa Zorro ya yi shugabancin Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta ƙasa, NUJ, Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Afirka-maso-Yamma da kuma tarayyar ‘Yan Jaridar Afirka,

“Zorro ya riƙe shugabancin kwamitin kula da harkokin ‘yan gudun hijira a Arewa-maso-Gabas lokacin yana ɗan majalisar wakilai”, inji Garba Shehu

Sannan ya sanar da sauyin wajen aiki na masu muƙaman siyasa uku daga ofishin Matar Shugaban Ƙasa zuwa ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya kafin daga bisani a kai su wasu hukumomin da ma’aikatun su ci gaba da aiki a can.