Tsohon gwamnan Ekiti, Fayose ya ɗare acaɓa a Legas

A wani mataki don gudun kada jirgin sama ya baro shi a tasha, ya sanya tsohon gwamnan jihar Ekiti Ayo Fayose, ya hau acaɓa zuwa babban filin jirgin sama na Murtala Mohammed da ke Legas.

Wani hoton gwamnan da ya karaɗe kafafen sadarwa, ya nuna yadda tsohon gwamnan tare da dogarinsa suka hau acaɓa guda don a kai su filin jirgin.

Tsohon gwamnan shi da kansa ya soma yaɗa hoton a shafinsa na facebook inda ya nuna matsalar cunkoson abubuwan hawa a Legas babu ruwanta da ko kai waye, wanda ala tilas ya zaɓi hawa acaɓa son jada ya rasa jirgi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *