Daga UMAR AKILU MAJERI a Dutse
Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Saminu Turaki ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar PDP.
Turaki ya bayyana hakan ne a ranar Litinin jim kaɗan bayan wata ‘yar gajeruwar ganawa da shugabannin jam’iyyar PDP ta Jigawa a gidansa da ke Kano.
Tsohon gwamnan ya ce ya yanke shawarar haɗa kai da tsohon gwamna Sule Lamido ne don fatattakar Gwamna Badaru da abokan siyasarsa daga gidan gwamnatin jihar.
“Na koma jam’iyyar PDP ne da nufin ciyar da jihar Jigawa gaba da kuma ƙwato mutanenmu daga mulkin kama-karya na APC.
“A matsayina na shugaba ban koma PDP ba domin in samu wani muƙami ba, zan yi iya ƙoƙarina na jagorancin jam’iyyar zuwa ga nasara a zaɓen 2023 mai zuwa,” inji Turaki.
A martanin da gwamnatin APC ɗin Jigawa ta mayar wa Saminu Turaki kuwa, ta ce da shi Allah ya raka taki gona, dama a cewarta Saminu Turaki bai tava zama ɗan Jam’iyyar APC ba, kuma jam’iyyar APC ba ta taɓa yunƙurin janyo shi cikin jam’iyyar ba, kamar dai yadda Kakakin gidan gwamnatin Jigawa Alhaji Auwal D. Sankara ya bayyana a madadin gwamnan jihar.
Sankara ya ƙara da cewa, Jam’iyyar All Progressives Congress (APC), jam’iyya ce ta ‘yan siyasa masu son ci gaba, saboda haka suna maraba da duk ‘yan siyasa masu kishin ƙasa, waɗanda a shirye suke su yi wa al’ummar Jigawa da Nijeriya hidima ba tare da son kai ba.