Tsohon Ministan Ƙwadago, Musa Gwadabe ya rasu yana da shekara 87

Fitaccen ɗan siyasa kuma tsohon Ministan Ƙwadago, Alhaji Musa Gwadabe, ya kwanta dama.

Majiya daga ahalin marigayin ta ce, tsohon Sakataren Gwamnatin Kanon ya rasu yana da shekara 87 bayan fama da rashin lafiya.

Majaiyarmu ta ce za a yi jana’izar marigayin ne ranar Laraba da misalin ƙarfe biyu na rana a gidansa da ke hanyar Ado Madaka a Maiduguri road, Kano.

Gwadabe ya rasu ya bar mata biyu, ‘ya’ya 11 da jikoki da dama. Daga cikin ‘ya’yan nasa akwai Alhaji Nazifi Musa Gwadabe da sauransu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *