Tsufa (3)

Daga MUSTAFA IBRAHIM ABDULLAHI

’Yan uwa masu karatu Assalam alaikum. Barkan mu da wannan lokaci; barkan mu da sake saduwa a wannan shafi mai albarka, wanda ke kawo muku bayanai game da jikin ɗan adam, domin ku fa’idantu, kusan yadda jikinku ke aiki.

Har yanzu dai , mu na  magana ne a kan tsufa. Muna bayanin sauye sauyen da shi tsufa ya ke kawo a sassan jiki na ɗan Adam. Yau zan ɗora daga inda na tsaya.

Shi tsufa ya na kawo raguwar fikira da azanci,  raguwar tsokar nama a jiki, ƙaruwar kitse a jiki, rauni a gaɓɓai, raguwar ƙarfin gudanar da ayyuka, bayyanar furfura, da kuma tsukewar hanyoyin ko magudanan jini. Idan har kuna biyo, na yi bayanin dukka waɗannan.

A satin jiya, na faɗa cewa:

  1. Garkuwar jiki ita ma ƙarfinta zai fara baya. Cutukan da take iya yaƙa a da lokacin da mutum ya ke matashi ko matashiya sai su nemi su fi ƙarfinta.  Idan kuma su ka samu rinjaye a kanta, sai mutum ya fara rashin lafiya. Wannan shi ne dalilin da yasa tsofaffi su ka saurin kamuwa da cututtuka daga ƙananan har zuwa manyan! Anan na tsaya yanzu zan ɗora.

Wani abin shi ne raguwar tsokar naman jiki da kuma ƙaruwar kitse kan haddasa raguwar ruwan jiki. Ruwan jiki abu ne mai matuƙar muhimmanci a rayuwar ɗan Adam, saboda duk wani abu da ke faruwa a jiki to ko dai a cikin ruwan jikin ya ke faruwa, ko kuma ruwan jikin ya zama sila na faruwar wannan abu. Saboda tsofaffi su na da ƙarancin ruwa a jikinsu, duk wata cuta ko wani mataki da jiki zai ɗauka Wanda zai rage ruwan jiki kan kefa tsoho colin matsala.  Ruwan jiki rubutu ne mai zaman kansa da zan kawo bayanin sa nan gaba kaɗan in sha Allah.

  1. Tsufa yana rage yawan ƙwayoyin halittu masu tace jini su samar fitsari waɗanda ake Kira “nephrons”. A cikin kowacce ƙoda, akwai waɗannan ƙwayoyin halittu sama da miliyan ɗaya. To da zarar mutu  ya ƙetare shekara 45 a rate, sai su fara raguwa a hankali a hankali. Amma hakan ba zai hana samar da fitsari ba, saboda su na da matuƙar yawa. Kamar da yadda na faɗa  a baya cewa suma ƙwayoyin halittar ƙwaƙwalwa suna raguwa a hankali a hankali Wanda hakan ke rage kaifin tunani da azanci, amma sai a ɗauki tsawon lokaci.
  2. Halittar ɗa namiji da ta ‘ya mace su ma tsufa bai kyale su ba. Misali, kuzari da lafiyar da ‘ya’yan rai na  maniyyin namiji su na raguwa yayin da shekarun shi namijin ke ƙaruwa. Maniyyin da namiji zai samar a lokacin yana matashi ɗan shekara 20 zuwa 45 ba zai kai ingancin Wanda zai samar ba a lokacin da ya kai shekara 50 zuwa 65, daga nan har zuwa shekaru su gangara ƙassam ingancin maniyyin zai ta raguwa ne. Ga siffar ‘ya’yan rai na maniyyi kamar haka: Duk ɗan rai na maniyyi ya na da kaim gangar jiki, da kuma jelyaa. Bincike masana nuna cewa girman namiji a shekaru Kan sa a dinga samun sauyi a wannan siffa ta ainihi. Za a dinga samun ‘ya’yan rai na maniyyi masu jela biyu, ko masu kai biyu, ko marasa jela, ko masu gajeriyar jela. Duk waɗannan ba za su iya sa wa mace ta ɗauki ciki ba. Haka kuma girman maraina ya na raguwa a yayin da shekaru su ka ja.

Akwai wani kuttu da ke jikin bututun mafitsarar namiji. Ana kiransa da “prostate”. Aikinsa shi ne tsarto da ruwa wanda ya kai kaso 30 cikin 100 na ruwan da ke maniyyi.  Da zarar namiji ya wuce shekara 40, wannan halitta ta na kumbura har ma ta Kan matse bututun mafitsara. Wannan shi ke kawo wahala da jin zafi ga manya maza yayin yi fitsari ko kuma inzali. Masana sun ce kimanin kaso 50 na maza na fama da wannan matsalar.

A ɓangaren mata kuwa, tsufa ba kawo ɗaukewar jini  al’ada. Lokacin da hakan ya fi faruwa shi ne yayin da mace ta kai shekara 50. Duk da cewa wasu matan Kan daina kafin shekara 50, wasu kuma sai sun ƙetare shekara 50. Shi yasa masana su ka ƙiyasta cewa lokacin shi ne daga shekara 45 zuwa 55. Mace za ta gane ta kai wannan mataki yayin da ta yi shekara guda cur bata ga baƙonta ba.

Rashin jini al’ada a tare ya ke da rashin zubowar wasu sinadarai masu shirya mahaifa domin ɗaukar ciki idan an sadu. Saboda haka da zarar an kai wannan mataki, mace ba za ta iya ɗaukar ciki ba, wannan a kimiyyance kenan. Saboda an samu matan da sun ƙetare wannan ƙadari na rayuwa amma Allah ya ba su rabo.

Kafin mace ta kai shekara 45, wato misali daga shekara 25 zuwa 35, lafiyar ƙwayayen da ta ke samarwa da kuma ƙarfin numfasawar da za ta iya yi lokacin naƙuda ya na raguwa a hankali a hankali. Shi ya sa mafi yawan lokaci, idan sai bayan da mace ta girma sosai sannan ta samu rabo, a kan sha wahala kafin a haife , a wasu lokutan ma sai dai ayi tiyata (CS), a ciro ɗan ko ‘yar.

Tasirin waɗancan sinadarai da muke kira da (hormones) a jikin mace, ya na da yawa. Rashinsu a sakamakon saukowar tsufa kan kawo raguwar sha’awa, raguwar ƙarfin ƙashi, da kuma shikawar matuci. Matsalolin bacci da sauyawar yadda mace ke ji a jikinta kan iya biyo baya.

  1. Ƙarfin ƙashi na raguwa yayin da mutum ke ƙara tsufa. Saboda raunin da ƙashi ya ke yi, wasu ma sai sun dogara da sanda sannan tafiya za ta yiwu. Za a samu ƙashi ya dinga zama mai yawan huda-huda daga cikinsa, wato abinda hausawa ke kira da tantanƙwashi. Amma akwai bambanci tsakanin maza da mata a wannan waje. Ƙashin mata ya fi zama mai “biskit”, ma’ana ya fi yin rauni fiye da ƙashin maza. Dalili kuwa shi ne su maza marainansu na samar da wani sinadari da ake Kira “testosterone” Wanda daga cikin ayyukansa akwai ƙarawa ƙashi ƙarfi da nagarta. Su kuwa mata kamar yadda na faɗa, su na rasa sinadaran da suka shafi halittarsu ta mata, saboda haka ƙashinsu ya fi saurin yin rauni bayan shekara 50. 

Abinda ya sa ƙashi ke yin rauni ya samo asali ne saboda jiki ya fara gajiya wajen tsame sinadarin da ke bawa ƙashi ƙarfi wanda mu ke samu daga abinci. Ƙasusuwan da su ka fi saurin yin rauni su ne: ƙashin cinya, musamman inda ya yi mahaɗa da ƙugu (tsofaffi sun fi karyewa a nan). Sai kuma mahaɗar wuyan hannu, da kuma ƙashin baya. Tun da an zo maganar ƙashin baya, ba ri na baku batu na goma.

  1. Ko kun san cewa tsufa da shekaru na rage tsayin ƙashin baya? A tsakanin ƙashi da ƙashi na gadon baya akwai wani guntsi mai basu tallafi kuma mai bamu damar iya sunkuyawa. Shekaru na sa wannan guntsi ya goge ya zama ɗan siriri,  ta haka sai tsawon mutum ya ragu. Akwai iron wannan guntsi a mahaɗar gwiwa kuma shi ma yana gogewa yayin da shekaru su ka ja. Shi yasa da za gwada tsayin mutum a lokacin yana ɗan shekara 25, sannan a sake gwada tsayin nasa bayan da ya kai shekara 60, tabbas za a ga bambanci.

Masu karatu, ku tara a mako na gaba, domin ci gaba da karanta bayani game da Jikin ɗan Adam. Kafin nan na ke cewa, wassalam alaikum.