Tubabbun mayaƙan Boko Haram sun gudanar da aikin share unguwanni a Maiduguri

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN a Maiduguri

Wasu tubabbun mayaƙan Boko Haram sun gudanar shara da tsaftace birnin Maiduguri, a ranar Asabar a yunƙurin da gwamnati ke yi na al’umma su sake amincewa da su, don ci gaba da rayuwa kamar yadda aka saba.

Cibiyar Cigaban Dimukuraɗiyya (CDC) tare da haɗin gwiwa da gwamnatin jihar Borno ne suka shirya aikin tsaftace muhalli da tubabbun mayaƙan suka aiwatar.

Da yake bayanin maƙasudin aikin, Malam Mustafa, babban jami’in gudanar da bincike a cibyar, ya bayyana cewa an ɓullo da wannan mataki ne a matsayin wani ɓangare na shirin mayar da tubabbun cikin al’umma don ci gaba da rayuwa kamar yadda aka saba.

“Maƙasudin da ya sanya CDD ta bai wa gwamnatin jihar Borno goyon baya wajen gudanar da wannan shirin shi ne domin jama’a su sake karɓar tubabbun hannu biyu.

“Muna da ƙudurin samun sauyin matsayi da kallon da jama’a suke yi wa sha’anin, musamman kallo maras kyau da al’umma suke da shi a garuruwa daban-daban.

“Saboda haka muna ƙoƙarin sake inganta alaƙa tsakanin al’umma da tubabbun mayaƙan a garuruwanmu,” inji Mustafa.

Har wala yau kuma ya bayyana cewa sun yi amfani da tubabbun mayaƙan kimanin 400 domin gudanar da aikin tsaftace muhalli tare da kimanin 50 a cikin su waɗanda aka fara aikin shara da su a Sansanin Alhazai da ke Maiduguri wanda ya ƙunshi kimanin tubabbun mayaƙan 12,000 da iyalansu.

Ya ƙara da cewa aikin tsaftace muhalli da tubabbun zai ci gaba faɗaɗa zuwa wasu yankunan birnin Maiduguri da sauran sassan birnin. Mustafa ya ce, an koyar da tubabbun dabarun kauce wa duk wani ƙalubalen da za su ci karo da shi.

A nashi ɓangare, mai taimaka wa Gwamna Babagana Zulum kan harkokin tsaro, Abdullahi Ishaq ya yaba wa ƙungiyar CDD bisa ga namijin ƙoƙarin ɓullo da shirin wanda zai taimaka sosai.

Ya shaidar da cewa, “sulhu alheri ne, wanda gwamnatin jihar Borno ta ƙirƙira bayan ɗaukar dogon lokaci ana fuskantar matsalar tsaro, wanda hakan ne ya taimaka mayaƙan Boko Haram da dama suka jingine makamai.”

Ya buqaci ɗaukacin al’ummar jihar Borno su yi na’am da shirin tare da bayar da cikakken goyon baya mai ma’ana wajen samun nasarar shirin.

Wasu daga cikin tubabbun mayaƙan, sanye da rigunan da aka rubuta cewa: “Ku yi mana afuwa ku yafe mana, mun tuba.” gefe guda kuma an rubuta: “Bari mu sake gina jihar Borno,” inda kuma suka buƙaci baki ɗaya al’umma su yafe musu tare da karɓarsu a matsayin tubabbun da suke da muradin zaman lafiya da cigaban jihar.