TUC ta buƙaci Shugaba Tinubu ya dakatar da cire tallafin mai

Daga BASHIR ISAH

Ƙungiyar ‘Yan Kasuwa (TUC), ta yi kira ga Shugaban Ƙasa Bola Tinubu da ya dakatar da manufarsa ta cire tallafin mai baki ɗaya.

Ƙungiyar ta ce mambobinta sun kaɗu matuƙa bayan da suka ji Shugaban ya ambaci batun cire tallafin mai yayin da yake jawabi jim kaɗan bayan rantsar da shi a ranar Litinin.

Da suke jawabi a wajen taron manema labarai da suka shirya ranar Talata a Abuja, Shugaban TUC na ƙasa, Festus Osifo da Sakatarensa Nuhu Toro, sun ce sun sa ran Shugaban ya zama wayayye game da matsalar da ke gaban ƙasar nan.

Osifo ya bayyana cire tallafin a matsayin babban al’amari wanda hakan ya sa tsohuwar gwamnati ta ƙi ɗaukar mataki a kan haka har ta miƙa wa gwamnati mai ci ragamar mulki.

Ƙugiyar ta ce duba da tasiri da kuma muhimmancin batun tallafin mai ga rayuwar ‘yan ƙasa, kamata ya yi a tafiyar da lamarin tare da lura.

Ta ƙara da cewa, ya dace a yi zaman tattaunawa da ba da shawarari kafin ɗaukar matakin cire tallafin baki ɗaya.

“Da wannan, muna kira ga Shugaba Tinubu da ya jinkirta domin ba da damar tattaunawa da shawarari kana a shigo da masu ruwa da tsaki…,” In ji ƙungiyar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *