Daga BELLO A. BABAJI
Ƙungiyar Kasuwanci, TUC ta yi kira ga jihohin da ba su fara biyan albashi da sabon tsarin mafi ƙarancinsa ba da su gaggauta aiwatarwa ko ma’aikatansu su shiga yajin aiki.
Shugaban ƙungiyar, Festus Osifo ya bayyana hakan jim-kaɗan bayan wani zama da Majalisar Zartarwarta ta gudanar a Abuja, a ranar Talata.
Ya nuna damuwa kan jinkirin aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi ga da dama daga cikin jihohin Nijeriya wanda hakan ke cigaba da haifar da tsaiko ga harkokin ma’aikata na yau-da-kullum.
Osifo ya bayyana cewa yayin da wasu jihohi suka cimma kaso 80 na zartarwar, wasu ko an bar su a baya, ya na mai bada misali da Jihohin Kuros Ribas da Zamfara.
A kwanan nan ne ma’aikata a Kuros Ribas suka je yajin aikin gargaɗi na kwana biyu wanda ya ce matuƙar ba zartar ba, to hakan ka iya haifar da na sai baba-ta-gani. Ya ce, akwai yiwuwar irin haka ya faru a Zamfara, ya na mai kira ga gwamnatocin jihohin da su yi ƙoƙarin kaucewa abin da zai biyo baya na yajin aiki.
Shugaban ƙungiyar ya yi kira ga gwamnatoci da su fifita walwalar ma’aikata ta hanyar shirya tattaunawa da ƙungiyoyin ƙwadago don samar da mafita game da lamuran albashi.