Tun ina firamare na fahimci ina da baiwar waƙa da rubutun fim – Abdulyasar C-19

“Fim mai dogon zango ne ya ba wa sababbin fuska dama a harkar fim”

Daga IBRAHIM HAMISU, Kano

Abdulyasar Aminu Abubakar da aka fi sani da Abdulyasar A. Abubakar C-19, wani fasihi ne da ya ƙware a ɓangaren rubutun fim da kuma umurni, a zantawarsa da wakilin Manhaja a Kano, za ku ji yadda ya fara da waƙar ‘Hip hop’ inda daga baya ya rikiɗe ya koma Darakta. Ku biyo mu, ku ji yadda hirar ta kasance:

MANHAJA: Za mu so ka gabatar mana da kanka ga masu karatunmu?

ABDULYASSAR C-19: Sunana Abdulyassar Aminu Abubakar, amma a kan kira ni da Abdulyassar A. Abubakar C-19.

Ko za ka ba mu taƙaitaccen tarihinka?

An haife ni a ranar Alhamis 6-3-1995 a cikin Jihar Kano a ƙaramar Hukumar Ungogo, ya zuwa yanzun Ina rayuwa a ƙaramar Hukumar Dala. Na yi karatun Arabi da Boko wanda karatun Arabi ɗin ya fi yawa. Tun Ina ajin ƙarshe na firamare na fahimci Ina da baiwar rubuce-rubuce kama daga waƙoƙi da rubutun zube sai kuma rubutun fim.

Mafi yawancin waƙoƙin da na rubuta waƙoƙin Hip Hop ne, wanda da Hausa ake ce musu Tsinbure, sai dai waƙar farko da na fara rera ta, Wakar Yabon Manzon Allah ce S.A.W. Na yi gwagwarmaya sosai a rayuwata ta fannoni da dama har ya zuwa dai yanzun da nake ci gaba da yin wasu kuma za mu ci gaba har ya zuwa yadda Allah ya so.

Ta yaya aka samu kaika a masana’atar fim ta Kannywood?

To, alal haƙiƙa zan iya cewa na tsinci kaina a masana’antar shirya fim ta Kannywood ban san lokacin ba, dalili kuwa a nan shi ne, na yi ta ja da baya kawai don ban so a gida a san Ina harkar fim, abin da nake kawo wa a raina shi ne, ana sani ɗin za a hana ni duba da kasancewar ana yi wa masana’antar wani kallo na rashin ɗa’a da suke da shi, ni kuma ni ne qarami a gidanmu. Na ci gaba da rubuce-rubuce wanda a lokacin ni da kaina na nemi wani Producer kuma jarumi a masana’antar na ba shi labarina na farko da na rubuta ‘Garba Mai Walda’, ya kuma min alƙawarin cewar zai ɗauki nauyin sa har ya ga ya fita. Alhandulillah kuma ya yi haka ɗin.

A wannan lokacin ma dai ban taɓa zuwa wajen inda ake ɗaukar fim ba. Nan Allah Ubangiji ya riqa haɗa ni da sanannun mutane wanda ni na riqa neman su, duk da Ina da wata dirka da in suka sanya ni gaba to la shakka zan kai bantena, amma na tsaya kan cewar ni zan nema da kaina gami da addu’a. Cikin hukuncin Ubangiji sai kuma na tsunduma kai tsaye, har ma na fara zuwa wajen ɗaukar fim inda a nan ɗin har na fara koyon ‘Continuity’, daga nan kuma sai abubuwa suka miƙa har ya zuwa yanzun.

Masana’atar Kannywood ta na da faɗi. Kai a me ka fi ƙwarewa?

Gaskiya abubuwan da na ƙware suna da yawa. Ina rubutu, Bada Umarni, kamara, a yanzun waɗannan abubuwan su na fi yi kuma a kowanne Ina da sani sosai a kai, domin da fari na shiga harkar fim ɗin ne da ka, sai na zo kuma na fahimci ai duniya ma da ilimi ta ke tafiya, har kullum kuma ni tunanina a kan na kawo sauyi ne.

Sai na tashi haiƙan kan neman ilimin meye ma fim ɗin da duk wani abu da na sanya gaba. Ban san iya adadin ‘Workshop’ da Semminna da na halarta ba wanda har Birnin Lagos na je na yi karatun fim na wasu watanni. Haka a nan Kano ma.

Wane fim ka fara rubutawa?

Fim ɗin da na fara rubutawa shi ne ‘Garba Mai Walda’, na rubuta shi ne a 2012 kuma a shekarar aka ɗauke shi, ma’ana aka yi fim ɗin.

A ɓangaren Bada Umurni fa, da wane fim ka fara?

Fim ɗin da na fara Bada Umarni sunan sa ‘Zamantakewa’.

Ya zuwa yanzu finafinai nawa ka rubuta ko ka Bada Umurni?

Na rubuta labarai da dama wanda aƙalla za su kai hamsin ko su haura. Na bada Umarni aƙalla finafinai goma su ma ko su haura.

Daga lokacin da ka fara zuwa yanzu waɗanne irin nasarori za ka iya cewa ka samu a harkar?

Na samu nasarori da dama wanda ba zan tava mancewa da su ba. Fim ya kaini inda ban tava tunanin zan je ba, ya haɗa ni da mutanen da ban taɓa tunanin zan haɗu da su ba, fim ya ba ni al’umma daga Jihohin Najeriya, Arewa da Kudu. Hatta wasu ƙasashen da ke maƙwabtaka damu sanadiyyar fim sun shigo cikin rayuwata.

Ƙalubale fa akwai ko babu?

Ƙalubale kam akwai shi domin a kan ce wai duk nasarar da ba ƙalubale a cikin ta to abar kallo ce. Ƙalubalen bai wuce na yadda jama’a suke kallon ka ba, alal misali, sukan ɗauka ne cewar duk wanda ke sana’ar fim walau mace ko namiji to ya fi ƙarfin iyayen sa ne, sun rasa yadda za su yi da shi.

A zahirin gaskiya kuma ba haka ba ne, zan iya cewa ma ni na fi wata macen tsaro a gidanmu. Dalili kuwa a nan shi ne, ko aboki na yi sai an san waye shi, haka idan aka ce ga wasu zan yi aiki da su, a zahiri na gaskiya ko mahaifina, ko yayyena sukan nemi waɗannan mutanen su san su waye su.

Kamar yadda a baya na ce ada Ina tsoron a san Ina harkar fim a gida za a iya hanawa, bayan sun sani, yayyena su suka shige gaba wajen iyayenmu suka ce da su, “matsawar ba karatu na bari ko aka ga zan bauɗe hanya ba, to a bar ni na yi tunda Ina da fasaha a wannan ɓangare” da yake iyayena masu saurin fahimta ne, suka yarje min.

Wane ne allon kwaikwayonka a ɓangaren Bada umurni?

S.S Rajamuli, marubuci ne kuma mai Bada Umarni a Ƙasar Indiya, har yau da muke wannan hirar da kai, ba na da na biyun sa a kowanne fanni da ka ji na ambata.

Ko za ka iya tuna wani fim da ya baka wahala wajen rubuta shi?

Fim ɗin da ya ba ni wahala wajen rubutawa shi ne, ‘Baiko 2022’. An taɓa yin fim ɗin a shekarar 2005, sai aka dawo da shi hannuna kan na sake rubuta shi, amma ana so ya fi na da tsari da tafiyar labari, gaskiya a wannan lokacin na sha matuƙar wahala domin kaso uku da rabi na wancan tsohon labarin sai da na aje shi a gefe, kaso ɗaya ne na ɗauka. To wannan labari ya wahalar da ni sosai da sosai

Wane abu ne yake vata ma ka rai a rayuwarka?

Babban abin da ke ɓata min rai bai wuce yadda al`ummarmu suke ganin gazawar mu ba wajen aiki. Mukan ɗauki tsawon lokaci wajen shirya fim, mun jure tsaiwa. Mun jure chajin kai, ba dare ba rana, amma wanda ya zauna ya kalle shirin da bai wuce awa guda ba ya zo ya kushe wannan shiri da muka shafe kwana da kwanaki muna yin sa. Wannan abu yana matuƙar sosa min rai ainun.

Wane abu ne ya ke faranta maka rai a rayuwarka?

Abin da ke fatanta min rai shi ne, kasancewata Musulmi tun daga tsatsona, iya wannan abin fahari ne a waje na. Sai gudan abin farin cikin shi ne, a duk sa’in da zan fita wajen ɗaukar fim iyayena sukan ce min a dawo lafiya, Allah Ya bada sa’a.

Tun da nake fita ban taɓa dawowa ba lafiya ko na rasa wannan sa’ar ba, iya wannan abin farin ciki ne. Haka nan abokan aikina muna zaune lafiya da su, kullum su ma fatan su gare ni Ubangiji ya yi min tagomashi da kyakkyawan abu.

Me C-19 ke nufi, kuma ta yaya ka samu laƙabin?

Hmm. C-19 na nufin Covid 19. Na sami wannan sunan ne cikin shekarar 2020, lokacin da wannan ibtila’i ya addabi duniya, Allah ya kare. To a gaskiya a wannan shekarar na yi finafinai da dama waɗanda suka yi tashe cikin wannan shekarar a ɗan tsakani, wannan ya sa wasu keɓantattu da ke jikina suka laƙaba min wannan suna. Tun ban so har na haƙura na bar musu. Ko fim aka kawo min da zan Bada Umarni, wajen Director sai a saka Abdulyassar A. Abubakar C-19.

Wacce shawara za ka bai wa mai sha’awar fara yin fim?

Shawarata ga wanda zai fara fim a yanzu ita ce, ya dage ya ga cewar sai ya yi, duk wani abu da ka ga an samu a rayuwa ba a samun shi ta sauqi ko daɗin rai, tilas ka wahalta masa.

Bangon littafin ‘Daga Ni Ne..’

Yaya kake kallon finfinan Kannywood adaidai lokacin da ake yayin fim mai dogon zango?

Alal haqiqa finafinai masu dogon zango dole a yaba musu domin sun zo a gavar da ake buƙatar su tunda a da can ana damuwa ne dai sai ka kai tukun a saka a fim. Ma’anar sai ka kai, ana amfani ne da sanin fuskar ka tukun za a saka ka a fim, ba ruwan kowa da ƙwarewar ka.

Yanzu kuwa ba wanda ke damuwa da sai da sananniyar fuska, matsawar an samu labari mai ƙwari, Jaruman da suka iya isar da saƙo, to ba ruwan masu kallo da fuskarka. Wannan shi ne cigaban da finafinai masu dogon zango suka kawo.

Batun aure fa?

Ba na da aure, amma cikin hukuncin Ubangiji ina nan da abar ƙaunata wacce nake da buri da fatar ta kasance abokiyar rayuwata akodayaushe.

Menene burinka a masana’atar Kannywood?

Burina shi ne, a ɗauki kowa ɗaya ne, a haɗe kai, babu nuna ɓangaranci. Kome aka yi a baya a mance da shi a fuskanci gaba. Sa’annan Ina da burin a ce yau masana’antarmu ta Kannywood ta shiga jerin su Hollywood da Bollywood in sha Allah.

Mun gode.

Ni ma na gode matuƙa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *