Tun Ina firamare na fara rubutu – Gimbiya Rahma

“Marubuta a dinga bincike kafin rubutu”

Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano

Sanannen abu ne, rubutun adabi ya ta shi daga hannun masu buga littafai zuwa yanar gizo, wanda hakan ne ya ba wa matasa damar baje basirarsu ba tare da tunanin fara neman kuɗin buga littafi ba. Ta dalilin hakan ya sa ake samun marubuta da yawa masu rubutu kuma mai ma’ana, hakan ya tabbatar da cewa, matasan marubuta na matuƙar ƙoƙari wurin samar da labarai da za su ƙayatar da masu karatu. Duk da cewa, an yi ammana rubutun intanet ba karɓe wa marubuta kasuwa ya yi ba, samar masu da dama ta yin cinikin littafansu ba tare da faɗuwa ba. Da yawa a cikin marubutan ɗab’i sun fahimci hakan har ma sun bi layin don samun romon canjin zamani. Wannan na ɗaya daga cikin ababen da suka ƙara gogar da marubuta masu tasowa, suke samun ƙarin gogewa da ƙwarewa, kasancewar an ce duk wanda ya riga ka kwana, to fa tabbas ne ya riga ka tashi. Shafin adabi na wannan mako ya ɗauko maku ɗaya daga cikin matasan marubuta da duniyar marubuta intanet ke yayi, kasancewar ta jajirtacciya a ɓangaren kawo labarai masu faukar hankali. A tattaunawar, mai karatu zai ji tarihin baƙuwar tamu, nasarorin da ta samu zuwa lokacin da ta fara rubutu da kuma abinda ya ja ra’ayinta ga tsunduma harkar rubutu. A sha karatu lafiya:

MANHAJA: Da wa muke tare?

GIMBIYA: Da farko kuna tare da Rahma Ahmad Muhammad, wacce aka fi sani da Gimbiya Rahma a ɓangaren rubutu.

Ko za ki ba mu taƙaitaccen tarihinki?

An haifeni a garin Kano, na yi makaranta tun daga firamare har zuwa sakandire haɗe da makarantar allo da islamiyya duk a cikin garin Kano.

Ta yaya aka samu kai a harkar rubutu?

Na fara harkar rubutun tun ina ƙaramar yarinya, lokacin Ina makarantar firamare.

Me ya na ki sha’awa ki ka shiga harkar rubutu?

Farkon fara rubutuna gaskiya sha’awa ce, daga baya sai abin ya rikiɗe ya koma son isar da saƙo ga al’umma.

Da wane littafi ki ka fara?

Cikakken rubutuna ya fara da littafin ‘Zamantakewa’, wanda na rubuta tun Ina aji ɗaya da ƙaramar sakandire.

Ya zuwa yanzu waɗanne littafai ki ka rubuta?

Littattafaina babban labari da gajere sun kai goma sha biyar zuwa ashirin.

Daga lokacin da ki ka fara zuwa yanzu waɗanne irin nasarori za ki iya cewa kin samu?

Gaskiya na samu tarin nasarori a harkar rubutu, irin nasarorin da baki ba zai iya misaltasu ba, tun daga suna, jama’a, kuɗi da karramawa. A silar rubutu na samu karramawa ta ‘certificate’ sama da guda ashirin daga mabambamta ƙungiyoyi, a kuma silar rubutun na shiga gasar rubutu tun daga ta zube zuwa ta waƙa, wasu na yi nasara wasu kuma ba ayi ba, duk da kasancewar itama kanta faɗuwar nasara ce.

Duk cikin nasarorin dana samu akwai wasu guda biyu, waɗanda na samu cikin shekarar 2022, kusan a tare domin bambancinsu tazarar watanni huɗu ne. Cikin watan march na zo ta ɗaya a gasar Tsuburin Gobir, wacce aka shirya domin taya Alhaji Aminu Alan waƙa murnar samun sarautar Sarkin Ɗiyan Gobir. Cikin ikon Allah kuma a watan July na zo ta uku a gasar waƙar da Gamayyar Marubuta da Mazanarta Waƙoƙin Hausa reshen Jihar Kano suka shirya. Bayan su akwai wasu tarin nasarorin da na samu ta silar rubutu masu yawan gaske.

Ƙalubale fa kin samu ko babu?

Kusan komai na wannan rayuwar ba ya yiwuwa sai tare da ƙalubale, kamar hakan ne ta fanni rubutu, na samu ƙalubale iri-iri waɗanda ba za su iya faɗuwa ba.

Wane ne allon kwaikwayon ki a rubutu?

Gaskiya ba ni da allon kwaikwaya a duniyar marubuta, sai dai akwai mutanan da rubutunsu ya ke burge ni, ko na ce salonsu wanda har na kan iya amfani da shi a nawa rubutun.

A wane ɓangare ki ka fi ƙwarewa a harkar rubutu?

Rubutu kusan ya tava kowanne fanni, musamman na zube. Wanda zan tsara ta fanni, zamantakewa, faɗakarwa, ilimantarwa haɗe da barkwanci da soyayya.

Bangon littafin ‘Cutar Numfashi’

Waccee shawara za ki bai wa mai sha’awar fara yin rubutu?

Shawara ga duk mai sha’awar fara rubutu, ya yi bincike kafin farawa, kar a yi rubutu da ka, musamman fanni da ya shafi shari’a, kiwon lafiya ko siyasa.

Kin taɓa barin Kano a kan harkar rubutu?

Ban tava barin Kano ba gaskiya.

Menene burinki a rubutu?

Babban burina a harkar rubutu, na ci gaba da cin gajiyarsa har ƙarshen rayuwata.

Tsakanin rubutun littafi da rubutun waƙa wanne ki ka fi yi?

Na fi yin rubutun littafi, domin ban cika rubuta waƙa ba, sai idan wani muhimmin abu ya zo mini da ya dace kuma na yi waƙe a kai.

Tsakanin rubutun littafi da na online wanne ki ka fi yi?

Rubutun online na fi yi, duk da tun asali rubutun ɗab’i shi ne muradina. To rashin mahaɗi ya sa na ke isar da saƙon ta ‘online’.

Muna godiya.

Ni ma na gode ƙwarai.