Tunisiya da Sin sun yi bikin miƙa Kwalejin Diflomasiyya da Sin ta gina

Daga CMG HAUSA

Ƙasashen Tunisiya da Sin sun gudanar da bikin miƙa sabuwar kwalejin diflomasiyya ta Tunisiya ta kafar intanet, wanda ƙasar Sin ta taimaka wajen ginawa.

Mataimakin ministan kasuwancin ƙasar Sin, Qian Keming, ya bayyana a lokacin bikin cewa, duk da mummunan tasirin annobar COVID-19, ƙasar Sin ta yi nasarar kammala aikin mai matuƙar inganci kuma cikin hanzari, lamarin da ya bada gagarumar gudunmawa wajen zurfafa hulɗar dake tsakanin ƙasashen da kuma ƙarfafa hadin gwiwa a tsakanin ƙasashen biyu.

Qian ya ce, Sin da Tunisia abokan hulɗar juna ne, wajen gina “shawarar ziri ɗaya da hanya ɗaya,” kuma ƙasar Sin tana son hada kai da Tunisia don yin aiki tare domin tabbatar da ci gaban ƙasashen biyu.

A nasa ɓangaren, ministan harkokin wajen ƙasar Tunisiya, Othman Jerandi, ya ce aikin gina kwalejin nazarin diflomasiyyar Tunisiya, an kammala shi a watan Disambar shekarar 2021, kamfanin gine-ginen ƙasar Sin ya gudanar da aikin cikin shekaru sama da biyu, kana aikin wata alama ce dake kara bayyana kyakkyawar hulɗar abokantaka tsakanin ƙasashen Sin da Tunisiya.

Fassarawa: Ahmad