Turawa na ɗaukar ado da kwalliya da muhimmanci – Khuraira Musa

“Ilimi da gaskiya za su iya kai mutum ga nasarar da ba ya zato”

Daga ABUBAKAR M. TAHEER

A yau shafin Mata A Yau ya yi wa mata tanadin firar da suka fi so, wato kwalliya da masu yin ta, inda muka samu tattaunawa da ƙwararriya a ɓangaren ado. Hajiya Khuraira Musa ‘yar Nijeriya ce da ta ke sana’ar ado da kwalliya a Ƙasar Amurka. Bafulatana ‘yar ƙaramar Hukumar Lere da ke Jihar Kaduna, sai dai ta girma a ƙaramar Hukumar Bassa dake Jihar Fulatu. A cikin wannan tattaunawa da wakilin Manhaja ya yi da ita, ta kawo Irin ƙalubale da ta fuskanta tun daga gida Nijeriya zuwa zamanta a Ƙasar Amurka tare kuma da irin nasarorin da ta samu. Ta sanadiyyar irin ƙalubalen rayuwa da ta fuskanta, Hajiya Khuraira ta rubuta littafi mai suna ‘Audacity Of Africa Girl’, don bayyana rayuwar da ta fuskanta a doguwar tafiyar rayuwa. A sha karatu lafiya:

MANHAJA: Za mu so ki gabatar da kanki ga masu karatunmu.

KHURAIRA: Assalamu alaikum. Sunana Khuraira Musa wanda aka haifa a ƙaramar Hukumar Lere dake Jihar Kaduna. Iyayena fulani ne, son haka muka taso a Rugar fulani, daga nan zama ya dawo da mu ƙaramar Hukumar Bassa dake Plateau State.

Na taso a hannun yayar mahaifina Hajiya Zainab, bayan rasuwar mahaifiyata a wurin haihuwa inda aka sakani a makarantan firamare ta Turawan mulkin Mallaka. Bayan kammala firamare an so a yi min aure, amma na qi wannan tasa ban yi sakandare ba.

Daga nan na samu na tafi babbar makarantar lafiya Health Technology inda na samu aiki matsayin maakaciyar lafiya. Bayan na yi aure, muka koma Kaduna da mijina, inda na samu damar zana jarrabawar sakandare GCE wanda haka ya bani damar tafiya Jami’ar Ahmadu dake Zaria na fara karantar Accountancy a shekarar 1990.

A lokacin an yi wani rikici wanda aka maida baƙi ƙasashensu haka tasa aka rufe jamioi wannan tasa nayi magana da maigidana inason tafiya Amurka cigaba da karatu ya kuma bani dama.

Na samu damar yin Leberal art da Business administration a can, na kuma karanci yadda ake yin ado da kwalliya.

Wannan tasa na samu gogewa sosai inda nake koyawa mutane ado da kwalliya a Calfornia daga baya na koma New York.

Da yake Allah ya hore min saurin gane abu, sai ya zama na fara shahara wajen yin kwalliya wanda nake zuwa garuruwa daban-daban da manyan shaguna Ina koya yadda ake siyar da shi kayan dama yima mutane suna biya na.

Na yi aiki da manyan kamfanoni na Amurka har guda 3, wanda manyan masu kuɗi da shahararrun matane suke zuwa inda na shafe kusan shekaru 12.

Su turawa suna son mutum mai basira da gaskiya, wannan tasa na samu damar shiga cikin masu kwalliya na duniya inda nake shiga Canada, England da ma manyan birane na Amurka. Sai ya zama na samu dama wajen taimaka musu muna ƙirƙirar kayan kwalliya na musamman ga baƙaƙen fata.

Duk wannan cigaban kina da aure a nan gida Nijeriya kika same shi?

Eh, to, ina da aure sai dai ba wancan na farko ba, bayan aurena ya mutu na Nijeriya, sai ya zama na samu na ƙara aure a can. Na kuma buɗe nawa kamfani inda nake koyar da yadda ake kwalliyar dama yima mutane kwalliya inda nake yi na kuma samu ɗaukaka sosai, gidajen jaridu da talabijin suka ban dama nake haska yadda nake aiki dama siyar da su. Bayan haihuwar ‘yan biyu sai na dena aiki da kamfanoni domin kula da iyalina. Hakan ya bani dama na buɗe shafi inda nake tallata kayan a ƙasashe daban daban ciki har da nan gida Nijeriya.

Yayanki nawa ya zuwa yanzu?

To Alhamdulillah. Ya zuwa yanzu Ina da ya’ya biyar, maza huɗu, mace ɗaya. Ina da jikoki biyu. Wasu daga ciki sun kammala digirinsu daga cikinsu, wasu suna yi, ƙaramin cikinsu shi ne yake sakandare, wanda yake da burin zama likita.

Waɗanne ƙalubale kika fuskanta a rayuwarki tun daga tasowa zuwa yanzu.

To gaskiya ƙalubalai akwai su tun daga maraici na rashin mahafiya da shiga makarantan, wanda firamarenmu wani Pastor ne yake koyarwa inda Anty Zainab ta yi ta tsoron kar na zama kirista, da kuma auren dangi, wanda na sha wahala a kansa, har kuma aka zo batun tafiya Amurka dama zaman a can. Haka kuma batun shi kansa karatu a Amurka na sha wahala da yake wanda na yi A Nijeriya turancin Engila ne. Amma Alhamdulillah na koya.

Haka Kuma ta fuskacin samun aiki da yake Ina baƙar fata, kuma ‘yar Nijeriya zai zama yanayin samun da bambanci da wanda yake ɗan asalin ƙasar. Amma Alhamdulillah na samu babu wani bata lokaci, kasancewar suna da wata ɗabi’a ɗaya, a lokacin da suka fahimci kana da baiwa to fa za su ba ka dama duk a inda ka fito.

Ko akwai wasu kyautuka da kika samu akan sana’arki?

To, gaskiya na samu kyautuka masu ɗimbin yawa, daga ciki akwai baƙar fata ta farko da ta iya kwalliya mai gaskiya, kyautar Mai iya koyar da Kwalliya, kyauta daga ƙungiyar mata masu ƙarfin faɗa aji ta duniya, dama kyautuka na tallafi da agaji da nake yi a nan Amurka dama ƙasata Nijeriya.

Dama kina da sha’awar rubutu ne ko kuma menene ya sa kika buga littafi mai suna ‘Audacity Of African Girl’.

To, maganar gaskiya wani yanayi ne na rashin lafiya da na yi a shekarar 2022, bayan fama da cutar Korona.

Ban tava tunanin zan rayu ba, sai na yi tunanin ya kamata na rubuta yadda na sha fama da rayuwa ganin na futo daga cikin talauci dama rashin gata.

Ka duba ni ɗin da aka saka a ƙwarya bayan haihuwata da kuma irin fama da kiwon shanu da na yi a jeji. Yau gani ana kallona a matsayin abar karramawa a Ƙamar Amurka, Canada, England wanda tasa naga ya kamata na rubuta ko bayan na mutu za a riƙa tunawa da ni kuma matasa musamman mata sun san irin gwagwarmayar da na yi har na kai ga cimma nasara.

Wane kira kike da shi ga matasa musamman mata ganin sun cimma burukansu na rayuwa?

Haƙiƙa Ina da kira ga mata wanda suka fito daga ƙauyuka da su dage wajen karatu domin samun cigaban rayuwarsu. Don an haifeka talaka ba shi yake nuna za ka mutu talaka ba. Karatu shine yake kai mutum matsayin da bai tava tunanin ba, haka kuma mutum ya yi riƙo da gaskiya a duk inda ya samu kansa ya kuma nemi waɗanda zasu ɗaga shi har ya kai ga nasara. Haka kuma mata su dage wajen neman na kansu koda ace suna gidajen mazajensu.

Da me kike tunanin za a tunaki a nan gaba?

Ina so a tunani a matsayin wanda ta ke da tunanin taimaka wa talakawa da marasa ƙarfi. Wannan tasa na koma ƙauyen da na fito, na gina makaranta domin tunawa da gudunmawar da Anty Zainab tamin na shiga makaranta.

Inda ake koyar da yara daga ƙabilu daban-daban, kyauta, domin tunawa da raɗaɗin talaucin da na fito a cikin sa.

Kenan kina da wata gidauniya ta tallafa wa marasa ƙarfi?

E Alhamdulillah, a yanzu kwanakin baya na buɗe wani organization mai suna ‘Arewa Development Support Initiate ASDI’. Wanda na haɗa ‘yan’uwa da abokanai masu hannu da shuni muke haɗa mafi ƙaranci Naira dubu biyu a shekara domin taimaka wa mata da matasa sana’oin dogaro da kai. A zuwa yanzu muna da sassa a jihohi 19 na ƙasar nan ciki har da babban Birnin Tarayya Abuja.

Daga ƙarshe menene kiran da kike da shi ga masu hali kan tallafa wa marasa ƙarfi.

Maganar gaskiya Ina da kira ga waɗanda Allah Ya ba su wani abu daga cikin arzikinSa, su tuna ba iyawar su ce ta ba su ba, don haka su dage wajen tallafa wa mutanen da ke da buƙata, ba kuma iya ‘yan’uwansu ba, duk wanda ka ci karo da shi da ke buƙatar taimako ka yi masa daidai iyawar ka, domin samun cigaba ga al’ummar gabaɗaya.

Mun gode.

Ni ma na gode.