Turmutsitsin rabon zakka a Bauchi: Adadin waɗanda suka mutu ya ƙaru

Daga BASHIR ISAH

Hukumomi a Jihar Bauchi sun ce, adadin waɗanda suka rasa rayukansu a wajen rububin karɓar zakka a Jihar Bauchi ya ƙaru.

A ƙarshen mako ne aka samu turmutsitsi a wajen wani rabon zakka lamarin da ya yi sanadiyar salwantar rayukan wasu da suka je karɓar zakkar.

Ya zuwa yanzu, mutum shida ne aka tabbatar da sun mutu bayan da aka ɗebe su zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa.

Kakakin rundunar ‘yan sanda ta Jihar Bauchi, Ahmed Wakilin ya tabbatar da haka sa’ilin da yake yi wa manema labarai ƙarin haske kan lamarin a ranar Litinin.

Jami’in ya bayyana waɗanda lamarin ya shafa da suka haɗa da:

  1. Aisha Usman ‘yar shekara 13 daga Gwang Gwang Gwang, Bauchi
  2. Sahura Abubakar ‘yar shekara 55 Anguwan, Bauchi
  3. Aisha Ibrahim Abubakar, ‘yar shekara 43 daga Hanyar Kobi, Bauchi.
  4. Khadija Isah, ‘yar shekara 8 daga Karofi, Bauchi.
  5. Maryam Suleiman, ‘yar shekara 20 daga Kandahar, Bauchi.
  6. Maryam Shuibu, ‘yar shekara 16 daga Gwang Gwan Gwan, Bauchi.
  7. Hassana Saidu, ‘yar shekara 53 daga Dutsen Tanshi, Bauchi.

MANHAJA ta rawaito lamarin ya faru ne a lakocin da mabuƙatan suka taru a harbar kamfanin Shafa Holdings Company Plc da ke kan hanyar Jos a garin Bauchi domin karɓar zakkar kuɗi na dubu goma-goma (N10,000) wanda wani bawan Allah ya fitar don raba wa jama’a.