Turmutsustun Ibadan: kotu ta bada belin waɗanda ake zargi kan Naira miliyan 10

Daga USMAN KAROFI

Babbar Kotun Jihar Oyo da ke Ibadan ta bayar da belin tsohuwar matar Ooni na Ife, Naomi Silekunola, da wasu mutum biyu, Oriyomi Hamzat, wanda shi ne shugaban gidan rediyon Agidigbo FM da ke Ibadan, da Abdullahi Fasasi, shugaban makarantar sakandaren Islamic High School. Ana tuhumar su da laifin kisan kai da rashin kula wanda ya yi sanadiyyar mutuwar yara 35 a lokacin wani taron kirsimeti a makarantar Islamic High School, Orita Basorun, Ibadan, ranar 18 ga Disamba, 2024.

A ranar 24 ga Disamba, 2024, an gurfanar da waɗanda ake tuhuma a gaban Kotun Majistare ta Iyaganku bisa tuhume-tuhume guda huɗu da suka haɗa da haɗin baki, kisan kai, sakaci, da kuma kisan gilla. Amma alƙalin babbar kotun Jihar Oyo, mai shari’a Kamorudeen Olawoyin, ya bayar da belinsu kan kuɗi Naira miliyan 10 kowanne, tare da shaidu biyu masu ƙarfi. Ya ce ba za a iya ci gaba da tsare su ba saboda babu wani tanadi a kundin tsarin mulki da ke ba da damar tsare su ba tare da yanke hukunci ba.

Mai Shari’a Olawoyin ya bayyana cewa lamarin wata tsautsayi ce ba tare da an yi nufin faruwar hakan ba. Ya kuma umarci waɗanda ake tuhuma da su miƙa takardun tafiye-tafiye na ƙasa da ƙasa (fasfo) ga kotu, sannan ya hana su yin wata hira da kafafen watsa labarai ko amfani da kafofin sada zumunta har zuwa lokacin da shari’ar za ta kammala