Daga IBRAHIM HAMISU
Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta ayyana Sanata Uba Sani na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen Gwamnan jihar Kaduna.
Sanata Uba Sani dai ya lashe zaɓen gwamnan ne da ƙuri’u 730002, sai mai bi masa na jam’iyyar PDP da ke da ƙuri’a 719196.