Umurah: Tawagar maniyyata ta farko daga Nijeriya za ta isa Saudiyya mako mai zuwa

*An bai wa yara sama da 13,000 shaidar izinin yin Umurah

Yayin da Umurah ta shekarar 1443 ke shirin somawa a ƙasar Sa’udiyya, ana sa ran maniyyata daga ƙasashen duniya su haɗu da ‘yan ƙasar wajen gabatar da ibadar.

Wannan ne ma ya sa tuni ofishin jakadancin Saudiyya a Nijeriya ya soma bai wa maniyya bisa ta hannun jami’ai masu kula da ɗawainiyar matafiya da aka tantance.

Haka ma kamfanonin jiragen sama su ma sun soma ba da bisar Umurah, inda ake sa ran jirgin fargo na jiragen da za su yi jigilar maniyyatan ya kwashi maniyyata zuwa ƙasa mai tsarki ya zuwa mako mai zuwa.

Ma’aikatar Hajji da Umurah ta Saudiyya ta ce, kawo yanzu ta bai wa yara ‘yan shekara 12 zuwa 18 sama da 13,000 shaidar izini (Permits) don ba su damar gabatar da Umurah da kuma kai ziyara Masallacin Annabi da ke birnin Madina.

Da yake jawabi kan batun, Mataimakin Ministan Umurah da Hajji na Saudiyya, Dr. Abdul-Fattah Bin Suleiman Mashat, ya ce an ba da izinin Umura ne ta hanyoyi guda biyu, wato ta manhajar Eatmarna da Tawwaklna, tsarin da aka inganta don kariya da kuma kare lafiyar maniyyata.

Ya ci gaba da cewa, ba a dawo da aikin Umurah ba sai da ma’aikatar ta yi aiki daidai da tsari tare da hukumomin da suka dace wajen ɗaukar matakan da suka dace domin samar da yanayi mai sukuni da zai bai wa maniyyata damar gabatar da Umurah cikin lumana.

Ministan ya nuna buƙatar da ke akwai a kiyaye duka ƙa’idodjin da ma’aikatar ta shimfiɗa domin kare lafiyar maniyyata da ta ma’aikata daga cutar korona.

A ƙarshe, ya yi kira ga jama’a da a yi amfani da manhajar Eatmarna da Tawwaklna wajen samun izinin Umurah.