UNICEF ta koka da ƙaruwar yi wa mata kaciya a Nijar

Yi wa mata kaciya na ci gaba da zama babbar matsala a fanin kiyon lafiyar al’umma, ɗiyaucinsu da kuma take haƙƙoƙinsu da ake yi ta wannan mummnar al’ada, lura da irin aika aikar da a hakan ke haifarwa ga ƙoshin lafiyarsu, sai dai abin baƙin ciki a Jamhuriyar Nijer wannan ɗabi’a maimakon raguwa sai ci gaba da ƙaruwa a cewar UNICEF.

Haka dai abin yake, idan ba a ɗau matakan da suka dace ba ‘yan mata miliyan 68 ne za su fuskanci kaciyar nan da shekara ta 2030 a duniya, kamar yadda wani bincike da hukumar yara ta Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya nuna.

Ranar yaƙi da yi wa mata kaciya da ake guddanarwa a ko wace ranar 6 ga wannan wata na Fabrairu a ko ina cikin duniya na nuna buƙatar ɗaukar ingantattun matakan yaƙi da al’adar kaciyar da ke zama cin zarafi tare da take babban haƙƙin ‘ya mace a duniya.

A cikin yankunan karkarar jamhuriyar Nijer, musaman a yankin yammacinta kashi 75.7% na matan da suka kama daga shekaru 15 zuwa 49 da haihuwa ne ake yi wa kaciya mafi yawansu kuma ana yi masu ne tun suna yan shekaru 5 zuwa 8 da haihuwa a cewar rayhoton na UNICEF.

Irin wannan kaciya ta yanke wani sashen matuntakar ‘ya mace an fi yin ta ne a yankin gabashin ƙasar ta Nijer. Haka kuma kashi 80 bisa 100 na kaciyar ana yinta ne da asaken gargajiya.

Domin ganin an dakatar da wannan mummunar al’ada, gwamnati da abukan hulɗarta na ci gaba da ƙara ƙaimi wajen wayar da kanun al’umma.

Kadidiatou Abdoulaye Idani, shugabar ƙungiyar matasa ‘yan mata ta fannin kiyon lafiyar haihuwa (AJFSR) ta bayyana bawin cikinta kan yadda ake ci gaba da samun yi wa mata kaciyar, musamman a yankunan karkara, inda sannu a hankali ta ke ci gaba da zama wani abin yayi.