UTME 2024: JAMB ta saki ƙarin sakamako 36,540

Hukumar shirya jarrabawar neman gurbin karatu a manyan makarantu (JAMB), ta saki ƙarin sakamako 36,540 na jarrabawar UTME da aka rubuta kwanan baya.

Ƙarin sakamakon ɓangare ne na sakamakon da hukumar ta riƙe don gudanar da bincike kan zargin tafka maguɗin jarrabawa.

Zuwa yanzu, adadin sakamakon UTME na ba bana da hukumar ta fitar, ya kama 1,879,437.

JAMB ta bayyana haka ne cikin sanarwar da ta fitar a ranar Talata ta bakin Kakakinta, Fabian Benjamin.

Sanarwar ta ƙaryata rahoton da aka yaɗa a soshiyal midiya kan cewa, hukumar za ta sake shirya jarrabawar sakamon wai an yi mata kutse ta intanet game da ragowar sakamakon da ke hannuta wanda take bincike a kai.

Hukumar ta buƙaci jama’a su yi watsi da wannan rahoto, tana mai cewa labari ne wanda babu gaskiya a cikinsa.