Uwa ta kai ɗanta kotu a Kano

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Masu iya magana na cewa, abinda ya koro ɓera ya faɗa wuta to ya fi wutar zafi. Wannan karin maganar ta yi daidai da lamarin da ya faru a Jihar Kano, yayin da mahaifiya, duk irin so da ƙaunar da uwa ke yi wa ɗanta, amma saboda wannan ya addabe ta, sai ta kai shi gaban alƙali domin a hukunta shi.

Mahaifiyar, wacce a ka sakaya sunanta, ta maka ɗan cikin nata a kotun shari’ar Muslunci mai lamba 1 da ke Ƙofar Kudu a birnin Kano ranar Talatar da ta gabata.

Cikin kuka, mahaifiyar ta shaida wa kotun cewa ɗan nata ya na ɗauko mata magana kuma ya na shaye-shaye matuƙa, sannan ya ƙi yin sana’a.

Ta ƙara da cewa, domin ta tserar da shi daga yin shaye-shayen, komai na rayuwarsa ta ɗauke masa iya daidai gwargwado amma duk da haka ya qi ya nutsu.

“Wallahi ko takalmin sa ne ya tsinke ni zan gyara masa ko na saya masa wani, amma ya ƙi ya daina shaye-shaye da ɗauko min magana.

“Ya sha cewa ya daina amma bayan kwana biyu sai ka ga ya dawo ruwa,” inji ta.

Daga bisani ne ta ke roƙon kotu da ta aike da shi gidan yari ko hakan zai sa ya kintsu.

Da alƙalin kotun, Munzali Tanko Soron-Ɗinki ya karanto wa matashin laifukan sa, sai ya amsa da bakin sa, inda ya nemi kotu da ta yi masa afuwa, ya kuma yi alƙawarin ba zai sake aikata munanan ayyukan ba.

Daga nan ne sai alƙalin ya bada umarnin a yi wa matashin bulala 30 sannan ya aike da shi gidan yari tsawon mako 2.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *