Uwa ta kashe aurenta ta auri saurayin ‘yarta a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU, Kano

Wata mata mai suna Khadijah dake zaune a Ƙaramar Hukumar Rano ta Jihar Kano ta kashe aurenta sannan ta auri saurayin ‘yarta.

Da fari dai, wani mai suna Usman ya nemi auren A’isha, wato ‘yar Khadijah, amma magabatanta suka nuna ba su amince da nagartarsa ba don haka suka hana auren, kamar yadda rahoton shirin ‘In Da Ranka’ na Freedom Radio, Kano ya bayyana.

Ana haka ne sai Khadijah ta ce ita fa ta amince da nagartar Usman, wato saurayin da yake neman ‘yar tata.

Hakan ya sa mahaifiyar A’isha ta kashe aurenta don ta auri Usman.

Iyayen Khadijah dai sun nuna ƙin amincewa da wannan aure da take so ta yi, abin da ya sa ta garzaya wajen Kwamandan Hisbah na Rano, inda ya ɗaura mata aure.

Waliyinta, Abdullahi Juma Rano, ya ce su fa ba su amince da wannan aure ba.

“Mu ba mu yadda ba, sai ta tafi wajen Kwamandan Hisbah na Rano suka yi ƙara. Kwamandan Hisbah ya kira miji, yana Mina, ta waya, ya ce lallai sai ya sake ta. Ya ce a shi ba zai sake ta ba. Shi ne Kwamandan Hisbah ya ce ya ba shi sati ɗaya.

“Da sati ya cika aka koma, saboda haka ya sake ta. Ita kuma da ma sun gama daidaitawa da saurayin ‘yarta a kan lallai sai ta kashe aure.

“Bayan ta zo ta kashe aure, ta je suka yi abin da za su yi, ta kawo mana shi gidanmu a kan mu ɗaura mata aure da shi. Muka ce mu. Muka ce mu mun san tun da aurenki yake neman ki, don haka mu ba za mu ɗaura miki aure da shi ba”, in ji Juma Rano

Naziru Juma Rano, wanda ɗan uwa ne shaƙiƙi, ya yi kira ga Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje da Kwamandan Hisbah na Jihar Kano, Sheikh Harun Muhammad Ibn Sina da su shiga maganar domin su a yanzu ma ba su san ina amaryar take ba.

Ita kuwa amarya, ta ce ita fa ta tambayi malamai a kan wannan auren nata kuma sun ce ba haram ba ne.

“Ni na tambayi malamanmu tun da sun ce ba haramun ba ne, amma ni ku tambaya mini. Aka tambaya aka ce ba haramun ba ne na zo na sanar da iyayen shi. Iyayen shi suka neme shi suka sanar da shi.

“Suka ce to ba matsala. Duk abin da suka gani shari’a bai saɓa wa abin ba saboda haka duk abin da suka ce shi zai yi,” a cewar Khadija