Daga JAMEEL GULMA a Kebbi
Uwargidan gwamnan Jihar Kebbi Hajiya Zainab Nasir ta buɗe wata cibiya don bayar da maganin ciwon tarin TB kyauta a garin Argungu.
Da ta ke buɗe cibiyar a wani sashe na babbar asibitin garin Argungu, Hajiya Zainab Nasir ta bayyana cewa yanzu an samo maganin ciwon tarin TB mai inganci ba kamar irin waɗanda cutar ke bijirewa ba.
Ana rasa rayuka da dama sanadiyyar ciwon da ake iya magancewa saboda halin ko-oho da mutanen da ke ɗauke da cututtukan ke nunawa wanda da sun dage da shan magani za su iya warkewa.
Ta ƙara da cewa za a kuma ɗauki mataki na hana tsangwamar masu dauke da cututtuka irin na tari wanda ba shakka zai ƙarfafa musu gwiwa wajen dagewa da zuwa cibiyar don karɓar maganin da zai iya raba su da cutar kwata-kwata.
Ta ƙara da cewa ba magungunan kawai aka tanada ba, an kuma tanadi na’urorin gwaje-gwaje na zamani kuma duk kyauta a ke yi tun kama daga gwaje-gwajen har zuwa bayar da maganin.
Malam Umar Bello Tambuwal babban jami’i ne daga ma’aikatar lafiya ta tarayya a sashen yaki da kuturta da tarin TB ya nuna jindadinsa bisa ga samarda wannan cibiyar da suka dade suna muradin samunta a jihar Kebbi tun shekarun baya.
Ya bayyana cewa kawo yanzu a ƙalla akwai yara sama da ɗari ɗaya da aka auna aka samesu da ciwon tarin TB aka killace su aka yi jinyarsu har suka warke sarai. Wannan cibiyar ta shahara wajen bayar da magungunan ciwon tarin TB musamman waɗanda ya yi tsananin da har ya kan bijirewa magani.
A nasa ɓangaren, kwamishinan lafiya na jihar Kebbi Yunusa Musa Isma’il ya yabawa uwargidan gwamna Hajiya Zainab Nasir da ma’aikatar lafiya ta tarayya da kuma masu tallafawa wannan aikin bisa ga yadda suka tsaya Kai da fata don ganin wannan cibiyar ta soma aiki.
Ya ce yanzu in Sha Allahu an daina ɗaukar masu wannan cutar zuwa yawon asibitoci a waɗansu jihohi.