Uwargidan Shugaban Ƙasa ta musanta shirin gudanar da addu’a ga ƙasa

Daga USMAN KAROFI

Uwargidan Shugaban ƙasa, Oluremi Tinubu da kuma mai ba Shugaban ƙasa shawara kan tsaro (NSA), Mallam Nuhu Ribadu a wata sanarwa an ce suna da hannu a wani shirin addu’o’i na kwana bakwai domin neman taimakon Allah a kan halin da ake ciki a ƙasar.

Rahoton da aka danganta wa daraktan babban tarayyar addu’a ta Ƙasa, Segun Afolorunikan, ya nuna cewa matar Shugaban ƙasa da Ribadu suna daga cikin waɗanda suka shirya shirin da aka sa wa suna “neman Allah ya shiga al’amuran Nijeriya .”

A cewar rahoton, Afolorunikan ya bayyana cewa wannan shiri za a gudanar da shi tare da haɗin gwiwar shugabannin addinai na Musulunci da Kiristanci a ƙasar.

Sai dai Busola Kukoyi, mai magana da yawun Uwargidan Shugaban Ƙasa, ta ƙaryata wannan batu a cikin wata sanarwa a ranar Asabar. Ta bayyana cewa, “Wannan shi ne domin fayyacewa da kuma sanar da jama’a cewa uwargidan shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ba ta shirya wani shirin Addu’a na Ƙasa ba.”

Ta kara da cewa, “Labarin da ke yawo a wasu kafafen yaɗa labarai na zamani ba su da tushe kuma kuskure ne. Saboda haka, duk wanda ya ci karo da wannan labarin ya yi watsi da shi. Uwargidan shugaban Ƙasa tana goyon bayan addu’a ga Nijeriya amma tana ganin cewa kowa yana da alhakin yin addu’a ga ƙasar ba tare da bambanci ba.”