Ɓacin rana: Attajiri Elon Musk ya tafka mummunar asara a dukiyarsa

Daga AMINA YUSUF ALI

Attajirin Biloniyan nan, Elon Musk ya tafka mummunar asara har ta zunzurutun kuɗi, Dala Biliyan 25 a cikin kwana guda rak!

Wato dai kamar yadda Hausawa kan ce, ‘wai ba kullum ake kwana a gado ba’. Al’amarin haka yake, domin Duniya juyi-juyi ce; watarana zuma, watarana kuma maɗaci. Wannan shi ne yadda za a fasalta al’amarin da ya wakana ga wannan attajiri Elon Musk. Mutumin da ya fi kowa arziki a faɗin Duniya.

Al’amarin ya faru ne sakamakon rashin samun kasuwa da attajirin ya yi a ƙoƙarinsa na sanya hannayen jarin kamfanin ƙera motocin nan na Tesla a kasuwa. Inda attajirin mai shekaru 50 da haihuwa ya fuskanci rashin kasuwar da bai taɓa fuskanta ba a tarihi. Abin da ya jawo ƙarfin arzikin Musk ɗin ya sauka i zuwa Dalar Amurka Biliyan 216 kacal.

Hannun jarin kamfanin na Tesla ya ruguzo ne da kaso 11% a ranar Alhamis ɗin nan da ta gabata bayan kamfanin ya ba da sanarwar cewa ba zai fito da sababbin samfurin motoci ba a shekarar nan ta 2022, sannan har yanzu ba alamar ya fara aikin ƙera wannan motar da ya ɗanɗana wa mutane zuma a baki da ita, wato motar nan mai amfani da lantarki wacce kamfanin ya alƙawarta kuma ake sa ran kamfanin zai sayar da ita a kan farashin Dalar Amurka $25,000, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

A taƙaice dai masu zuba hannun jarinn ba su ji daɗin yadda suka samu wannan sanarwa daga kamfanin ba. Ta cewa ya fasa waɗancan alƙawurra. Don haka, da yawa suka janye hannayen jarin nasu.

Idan za a iya tunawa, attajiri Elon Musk a shekarar 2021, yana da ƙarfin arIkin da ya kai Dalar Amurka biliyan $273.5, abin da ya ba shi damar mutum ma fi arziki a Duniya. Sai kuma mamallakin Amazon, Jeff Bezos yake rufa masa baya. Wanda yake da Dalar Amurka, biliyan $194. Sai kuma Ciyaman ɗin LVMH, Bernard Arnault da yake da Dalar Amurka, $177.