Vision FM: BON ta buƙaci NBC ta sassauta hukuncinta

Daga BASHIR ISAH

Hukumar gidajen rediyo da talabijin ta ƙasa (BON) ta ce, matakin da NBC ta ɗauka a kan tashar Vision FM, na ƙaƙaba mata harajin Naira miliyan biyar tare da dakatar mata da shirin ‘Idon Mikiya’ na tsawon wata shida ya yi tsauri da yawa.

BON ta bayyana haka ne cikin wasiƙar da ta aike wa NBC game da matakin nata a kan Vision FM mai ɗauke da kwanan wata 14 ga Fabrairu, 2022 da kuma sa hannun sakatarenta, Dr. Yemisi Bamgbose.

BON na mai ra’ayin cewa ɗaukar irin wannan tsattsauran mataki kan wata tasha ka iya zama barazana ga cigaba da kuma ɗorewar kafafen yaɗa labarai a ƙasa.

Tana mai cewa, matakin ya saɓa wa ƙudurin NBC na bai wa tashoshi haɗin kai, ƙarfafa musu gwiwa da kuma ba su kariya gami da tabbatar da suna gudanar da harkokinsu daidai da doka.

BON ta yi amfani da wannan dama wajen kira ga NCB da ta sake duba lamarin da idon basira don sulhuntawa cikin lumana wanda hakan zai taimaka wajen kare haƙƙoƙin kafafen yaɗa labarai.

Haka nan, ta bukaci NBC da ta buɗe ƙarin ƙofofin zaman tattaunawa a duk lokacin da lamari irin wannan ya taso don samun daidaito.

Idan dai za a iya tunawa, a kwanakin baya ne NBC ta ɗora wa Vision FM tarar Naira miliyan biyar tare da dakatar da shirin tashar mai taken ‘Idon Mikiya’ saboda tattaunawa da aka yi ta cikin shirin na Idon Mikiya kan batun badaƙalar tsawaita wa’adin aiki na shugaban hukumar NIA lamarin da NCB ɗin ta ce hakan ya saɓa wa dokokinta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *